Zagaye na biyu na zaɓen ´yan majalisar dokokin janhuriyar Kongo | Labarai | DW | 05.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zagaye na biyu na zaɓen ´yan majalisar dokokin janhuriyar Kongo

A yau ake gudanar da zagaye na biyu na zaben ´yan majalisar dokokin janhuriyar Kongo, inda ake takarar kujeru 84 a wannan kasa makwabciyar JDK. A zagayen farko na zaben wanday a gudana a ranar 24 ga watan yuni, jam´iyar Labour ta shugaban kasa Dennis Sassou Nguesso ta lashe kujeru 50 daga cikin 53 da aka yi takara kan su. To sai dai an tabka magudi a zaben. Ko da yake kasar ta janhuriyar Kongo mai yawan al´uma miliyan 4 ta na da arzikin man fetir amma daukacin mutanen ta na fama da mummunan talauci.