Zagaye na biyu na zaɓen shugaban Guinea | Labarai | DW | 28.07.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zagaye na biyu na zaɓen shugaban Guinea

Cellou Diallo ya fara samun goyon bayan wasu 'yan takara domin shiga zagaye na biyu na zaɓen shugaban kasa

default

Cellou Dalein Diallo

Ɗan takarar da ya zo matsayi na ukku a zagayen farko na zaɓen shugaban ƙasar Guinea daya gudana Sidya Toure, ya bayyana bayar da cikakken goyon bayan sa ga ɗan takarar da ya zo na farko a zaɓukan, wato Cellou Dalein Diallo wanda kuma zai fafata da ɗan takarar da ke rufa masa baya a yawan ƙuri'u kana jagorar 'yan adawar ƙasar Alpha Conde.

Sidya Toure dai ya kasance ɗan takarar da ka iya zama wanda zai tantance mutumin da zai yi nasara a zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasar da zai gudana bayan da ya samu fiye da kashi 13 cikin 100 na yawan ƙuri'un da aka jefa a sakamakon zagaye na farko na zaɓukan watan Yunin daya gabata. A cikin sakamakon dai Cellou Dalein Diallo ya sami fiye da kashi 43 cikin 100 ne da ƙuri'un.

Majiyoyin da suka fito daga jam'iyyar UFDG ta Diallo sun nunar da cewar, idan har ya yi nasara, to kuwa ta yi alƙawarin baiwa jam'iyyar Toure muƙamin Firaminista, da kuma kashi 30 cikin 100 na muƙaman ministoci a matsayin tuƙuici ga goyon bayan da ya bayar. Jam'iyyar ta kuma ƙara da cewar ɗan takarar daya zo matsayi na shidda a zaɓen shugaban ƙasar, Ibrahima Abe Sylla, shi ma zai bayyana goyon bayan sa ga Diallo wanda ya taɓa riƙe muƙaman minista da kuma Firaminista a ƙarƙashin mulkin tsohon shugaban ƙasar marigayi Lansana Conte.

Hukumomi a ƙasar ta Guinea dai basu kai ga sanya ranar gudanar da zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasar ba.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Ahmad Tijani Lawal