Zabtarewa ƙasa da Ruwan sama ya haifar da mutuwar mutane fiye da 200 | Labarai | DW | 09.04.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zabtarewa ƙasa da Ruwan sama ya haifar da mutuwar mutane fiye da 200

Kimanin mutane 200 ake kyautata zaton sun rasu yayin zabtarewar ƙasa a Brazil

default

Shugaban Brazil Luiz Inacio Lula da Silva

Kimanin mutane 200 ake kyautata zaton sun rasu yayin zabtarewar ƙasa sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a kusa da Birnin Rio de Janeiro na Brazil.

Yanzu haka masu aikin ceto na aiki ba dare ba rana domin gano masu rai da taɓo ya bizne musamman a wasu anguwannin marasa galihu dake kusa da Rio de Janiero.

Ko'a jiya sai da aka tono wasu mutane 25 da suka haɗa da ƙananan yara takwas, bayan sun shafe kwanaki da  dama a cikin taɓo.

Yanzu haka dai akwai mutane dubu 14 da suka rasa matsugunansu a sakamakon wannan bala'i. Ƙasar Brazil dai na ɗaya daga cikin ƙasashen duniya da akafi samun ruwan sama a duniya.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Zainab M. Abubakar