Zabiya a Afirka: "Suma ba su tsira ba!"
Ana nuna musu wariya da kyama da cin zarafi. Zabiya a Afirka kullum na cikin tashin hankali. Sai dai tilas hakan ya sauya. A cewar wasu Zabiyan da ke fuskantar kyamar da nuna wariya. Wannan misali ne mai karfafa gwiwa.
Fari abu ne mai kyau!
Thando Hopa daga Afirka ta Kudu wanda ke shekarunta na 20 a duniya Lauya ce. Tana sanya dogayen kaya da kuma abubuwan da za su kare ta daga hasken rana. A yanzu tana yaki da kyama da wariyar da ake nuna wa Zabiya a Afirka ka'in da na'in. Tana tallata kayan kwalliya ko kayan sawa da wasu kamfanoni ke yi, ta hanyar yin tafiyar nuna kwalliya a bainar jama'a.
Dandalin tafiyar nuna kwalliya
Shekaru hudun da suka gabata, Thando Hopa ta gano wata mai dinkin kayan kwalliya Gert-Johan Coetzee a cibiyar kasuwanci a Afirka ta Kudu, wacce ke tsaye a gefenta. A yanzu ta zamo daya daga cikin wadanda suka yi fice wajen nuna kwalliya a Afirka ta Kudu. Ana iya ganinta a shafukan mujallun tallan kayan kwalliya. Misali a bangon mujallar Forbes Life Africa ta tallan kayan ado, a shekara ta 2003.
Tilon 'yar gwagwarmaya
Yaki da cin zarafi na da saukin fada a baka fiye da a aikace. 'Yan Afirka da dama na ganin Zabiya ba su da amfani a rayuwa, suna musu kallon fatalwa. An camfa bangarorin jikinsu da cewa suna janyo baiwa da nasara. Zabiya matsalar kwayar halitta ce da ake samu a fata. Akalla ana samun mutum guda cikin 20,000 da aka haifa a duniya da wannan matsala. A Gabashi da Kudancin Afirka, ana camfa Zabiya.
Kisa sakamakon camfi
Miyagu na kashe Zabiya tare da sayar da sassan jikinsu ga malaman tsubbu. Majalisar Dinkin Duniya ta nunar da cewa sassan jikin Zabiya na kaiwa sama da 60.000 na kudin Euro a kasuwannin bayan fage. Ana sayar da kafa guda ta Zabiya Euro 2000. Tanzaniya dai ta haramta ayyukan malaman na tsubbu. Sai dai a kasashe da dama, misali Malawi har yanzu ba a haramta ba.
Zama cikin yanayi na tsoro da fargaba
Dorothy Mausen 'yar gundumar Machinga a kasar Malawi, ba ta da nutsuwa. A kasar da ke yankin Kudancin Afirka, akwai kimanin Zabiya 10.000. Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International, ta bayyana cewa cikin shekara guda da rabi da suka gabata, an hallaka akalla 18 daga cikinsu. 'Yan sandan Malawi sun sanar da samun rahotanni sama da 60 na cin zarafin Zabiya. Adadin zai iya fin haka.
Ko da yaushe cikin taka tsan-tsan
Razik Jaffalie ba ya taba barin dansa shi kadai. A kokarinsa na kare Cassim mai shekaru uku a duniya, ya hakura da aikinsa. Al'ummar Malawi na alfahari da kasancewarsu cikin zaman lafiya da kaunar juna. Sai dai dangane da batun farwa Zabiya, ko da shugaban kasar Peter Mutharika a wata hira da ya yi da manema labarai, ya ce yana jin kunyar abin da ke faruwa a kasarsa.
Waka ga Mandela
Salif Keita fitacce ne a bangaren kidan Pop a Afirka. An haife shi a kasar Mali, ya kuma san yadda rayuwar Zabiya ke cikin wahala a Afirka. A shekarar 1984 Keita ya tafi birnin Paris. Ya yi fice a yayin da ya bayyana a filin wasa na Wembley a birnin London, ranar 11 ga watan Yuni na shekara ta 1988, yayin bikin cikar Nelson Mandela da a wannan lokaci yake tsare a gidan kaso, shekaru 70 a duniya.
Babu gazawa, sai karfin hali
An gudanar da wani biki da na kwarya-kwaryar 'yanci a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango a shekarar 2015 mai taken: "Fièrement Ndundu". Taron kwanaki uku a Kinshasa, an yi shi ne da nufin musayar ra'ayoyi kan kalubalen da suke fuskanta da kuma karfafa gwiwar juna. 'Yan Afirka da dama na yin irin wannan gangami a kafafen sadarwa na zamani. Misali gangamin "#AlbinismisJustAColour" a shafin Twitter.
Taka tsan-tsan saboda rana!
Matsalar Zabiya ba wai kawai a launin fata ba ne. Basu da kwayar hallitar da ke kare mutum daga zafin rana, sannan za su iya kamuwa da cutar sankara cikin sauki. Dangane da haka suna fuskantar matsaloli masu yawa. Basu da kwayar hallitar da ke kare idanu ma. Hakan na nufin tilas ne su nemi abin da zai kare su daga hasken rana domin su rayu.
Yaki da nuna kyama ko wariya
Ana fara bayar da horo ga Said Seremani da sauran 'yan kungiyarsu ta "Albino United" in rana ta fara sanyi a birnin Daressalam. Ko da yake suna da karamin filin wasa, amma suna da babban fata. Suna son zama fitattun 'yan kwallon kafa na kasa da kasa irin su Didier Drogba ko kuma Pierre-Emerick Aubameyang.