ZABEN YAN MAJALISUN DOKOKI NA KUNGIYYAR EU A KASASHE 25. | Siyasa | DW | 13.06.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

ZABEN YAN MAJALISUN DOKOKI NA KUNGIYYAR EU A KASASHE 25.

HOTON TUTOCIN KASASHE 25 NA KUNGIYYAR EU .

default

Hausawa dai kance rana bata karya sai dai uwar diya taji kunya. Yau lahadi itace rana ta karshe da aka kammala zaben yan majalisu ko kuma wakilai na majalisar kungiyyar Tarayyar Turai wato Eu, a kasashe mambobi 25 dake cikin kungiyyar.

Zaben da aka fara a wasu kasashe uku na kungiyyar ta Eu a tun ranar alhamis din data gabata kawo yau lahadi,wadanda suka cancanci yin zaben a wadan nan kasashe 25 su a kalla miliyan 350 zasu zabo mutanen da zasu wakilci kasashen nasu ne a kujeru dari 732 a majalisar kungiyyar ta tarayyar turai dake da babban ofishinta´a kasashen Belgium da faransa.

Yan takara dai dubu goma sha hudu da dari 700 ne ke neman kujerun 732 a majalisar ta kungiyyar ta Eu na tsawon shekaru biyar.

Kamar yadda bayanai suka nunar wadan nan yan majalisa nada muhimmiyar rawa da zasu taka wajen dukkannin matakan da za a aiwatar a kungiyyar ta Eu,kama dai daga kasafin kudi da tsare tsaren yadda za a kashe su ta hanyar sufuri da kwadago da kuma muhalli.

Kasar Biritaniya da Holland na daga cikin kasashen da suka fara zaben a ranar Alhamis din data gabata. Kasar Czech da ireland kuma daga ranar juma,a. Kasashe irin su Italiya da Latvia da Malta na daga cikin kasashen da suka fara a ranar asabar din data gabata. Ragowar kasashen kuma 18 sun fara zaben nasu ne a safiyar yau Lahadi.

Ata bakin John Palmer masanin harkokin siyasa a kungiyyar ta Eu,cewa yayi daga dukkannin alamu masu kada kuri,u a wan nan zabe na yau ka iya yin amfani da wan nan damnar wajen bawa gwamnatocin su mamaki ta hanyar kin zaben jamiyyun nasu.

A yanzu haka dai biri yayi kama da mutum domin kuwa sakamakon daya fara fitowa daga kasar Biritaniya ya nunar da cewa jamiyyar Labour Fati ta Faraminista Tony Blair tasha kashi da kashi 26 daga cikin dari.

ita kuwa jamiyyar masu raayin rikau wato Conservatives nada kashi 30.Jamiyyar masu sssaucin raayi ta Liberals itace keda rinjaye da kashi 38 daga cikin dari.

Kafofin yada labarai na kasar Biritaniya dai sun rawaito cewa jamiyyar Labour ta Faraminista Tony Blair tasha kashi ne bisa irin jajircewa da Blair yayi wajen marawa kasar Amurka baya na kaiwa iraqi harin soji.

Hasalima tun kafin gudanar da zaben shi kansa Tony Blair ya fito fili ya nuna rashin tabbas na samun nasara daga jamiyyar sa ta Labour Fati bisa dalilin irin goyon bayan da yake bawa kasar Amurka,musanmamma a lokacin yakin na iraqi.

A waje daya kuma sakamakon zabe a nan tarayyar Jamus ya nuna a fili irin kayen da akayiwa jamiyyar SPD ta shugaba Gerhard Schroder,domin kuwa a karshen zaben ta buge ne da samun kashi 23 a cikin dari a maimakon abin da ta samu a zabe na baya da aka gudanar shekaru biyar da suka gabata.

jamiyyar adawa ta CDU da CSU ta hadaka ta samu gagarumin rinjaye da kashi 46 da digo 5 duk kuwa da cewa ta yiwo kasa idan aka kwatanta abin da ta samu a zabe daya gabata.

Jamiyyar za greens dake cikin gwamnatin hadaka da jamiyyar shugaba Schroder kuwa ta samu kashi 10 daga cikin dari wanda hakan ke nuna ci gaba data samu idan aka kwatanta kashi 6 da digo hudu data samu a zaben daya gabata.

Rahotanni daga tarayyar Ta Jamus sun nunar da cewa jamiyyar ta Shugaba Schroder tasha kaye ne bisa kukan da yan kasar keyi na rashin daukar matakan ragewa al,ummar kasar biyan haraje haraje a waje daya kuma da karuwar rashin aikin yi a cikin kasar.

Sakamakon zaben kuwa daga makociyyar kasar ta Jamus wato kasar Holland ya nunar da irin kaye ne da jamiyyar masu sassaucin raayi ta kasar ne tayiwa jamiyyun hadaka da faraminista Jan Peter Balekenende kewa jagoranci ne a kasar a yanzu haka.

To amma duk da wan nan kaye kafofin yada labarai na kasar sun rawaito faraministan na murna bisa irin yadda masu zabe suka fito kwansu da kwarkwatar suka kada kuriun nasu a wan nan rana ta zaben.

A kasashe kuwa irin su Latvia da kuma kasar czech bayanai sun nunar da cewa jamiyyun adawa na kasar sune suka lashe zabubbukan yan majalisun dokokin na kungiyyar ta Eu da gagarumin rinjaye.

A kuwa ta bakin masu nazarin siyasa a nahiyar ta Turai hasashe sukayi da cewa akwai alamun cewa gwamnatin masu raayin rikau dake mulki a faransa karkashin Jacque Chirac zata sha kashi a hannun jamiyyar masu sassaucin raayi ta Socialist,bisa wasu matakan kwaskwarima kann kudin fensho da gwamnatin ta zartar wanda bai samu amincewar da dama daga cikin alummar kasar ba.

Har ila yau masu sharhin siyasar na ganin cewa jamiyyar Silvia Berlusconi a italiya da alama itama zata sha kaye a wan nan zabe na yau,ba kuwa don komai ba sai don irin goyon bayan data dinga bawa Amurkas a lokacin yakin kasar iraqi.

Ita kuwa jamiyyar masu sassaucin raayi dake mulkin kasar Spain karkashin faraminista Jose Luis Zapatero bisa hasashen masu nazarin siyasa da alama itace zata kara lashe wan nan zabe na yau da gagarumin rinjaye tamkar dai abin da ya faru a kasar a zaben da aka gudanar watanni uku da suka gabata.

Wan nan hasashen nasarar jamiyyar ta Zapatero a cewar masu sharhi nada alaka da matakin da gwamnatin sa ta dauka ne na janye sojin kasar daga kasar iraqi.

A can kuwa kasar Girka sakamako ya nuna cewa jamiyyar NDP ta shugaba Costas Caramanlis ce ta lashe zaben da kashi 42 da digo 5 cikin dari. Inda ta bar jamiyyar adawa ta socialist da kashi 35 cikin dari. Jamiyyar yan kwaminist ta kasar kuwa nada kashi goma.

A gaba daya dai bayanai sun nunar da cewa an samu rashin fitowar masu kada kuri,a yadda ya kamata a kasashe irin su Slovenia da Faransa da Estonia da Latvia da Poland da Jamus kuma kasar Cezch.

A dai wani lokaci ne kadan a yau din nan ragowar sakamakon zaben a kasashe irin su Austria da Belgium da Cyprus da Denmark da Finland da Hungry da Lithunia da Luxembourg da Portugal da Slovakia da sweden da Spain da Poland da Austria zai kammala fitowa.

Wan nan zabe dai na yau a cewar masana ilimin siyasa babu shakka shine zai zama danba na aza harshahin cin nasarar zabubbuka a cikin wadan nan kasashe 25 mambobi a kungiyyar ta Eu a nan gaba idan Hakan ta taso.

IBRAHIM SANI.