Zaben yan majalisun dokoki a Kongo | Labarai | DW | 24.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben yan majalisun dokoki a Kongo

Al´ummomin kasar Kongo sun gudanar da zaben yan majalisun dokoki a yau lahadi.

Saidai jam´iyun adawa sun karacewa wannan zabe, a dalili da abun da su ka kira arigizon kuri´u, da shugaba Denis Sassou NGuesso ya shirya, da zumar samun gagaramin rinjaye.

Rahottani daga kasar sun nunar da cewa, a birnin Pointe Noire da Brazaville, mutane ba su hito ba da himma a rufunan zabe, sannan a wurare da dama , an fara zaben tare da jinkiri mai yawa.

Baki daya, yan takara fiye da dubu daya su ka shiga wannan zabe.

Kungiyoyin fara hulla, a kasar, sun hango cewar , zaben ba shi da wani armashi, ko da ya samu halartar jam´iyun adawa, ta la´akari da matakan da gwamnati ta dauka na tabka magudi, da nufi samun gagaramar nasara.