Zaben yan majalisun dokoki a kasar Iraki | Labarai | DW | 14.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben yan majalisun dokoki a kasar Iraki

A kasar Iraki gobe idan Allah ya kai mu a ke zaben yan majalisun dokoki, na gama gari.

Mutane kimanin ,million 15 da rabi, za su hito domin zaben yan majalisa 275, daga jimmilar yan takara 7655, bisa tsatsauran mattakan tsaro.

Tun ranar litinin da ta wuce, a ka fara zaben,tare da yan malati da yan kurkukun, da kuma jami´an tsaro.

Sannan, ranekun talata da laraba, yan Iraki mazauna kasashen waje su ka gudanar da na su zaben.

Wannan zabe, na matsayin matakin koli na girka demokradiya a kasar Iraki.

Sabuwar Majalisar da za a girka, ke da yaunin zaben shugaban kasa, da mataimaka 2, da kuma Pramista.

Akwai alamun a gudanar da zabukan na gobe, cikin sassauci tashe- tashen hankulla, a sakamakon kiran da kungiyar Jihadil Islami ta yi, da kuma jagororin yan sunna, na bukatar kar a kai hare hare ga runfunan zabe.

To saidai, kungiyar Alka´ida, ta ce maganar sassauci ba ta ma taso ba.

Tunni, hukumomi sun bada umurnin rufe iyakokin kasar, da shaguna , da opisoshi , da kuma hana zirga zirga.