1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben yan majalisun dokoki a kasar Irak

Dakaraun kungiyar Jihadil Islami a kasar Iraki sun yi kira, ga magoya bayan su da kar su ka kai hare hare a rufunonin zaben ranar alhamis mai zuwa a zaben yan majalisun dokoki, da za ayi.

Saidai wannan mataki inji sanarwar kungiyar ba ta nufin Jihadil Islami na nuna goyan bayan ga haramtacen zaben.

Ta yanke shawara hakan ne kawai domin kare rayukan talakawa bayi Allah da ba su ci kasuwa ba, rufuna ke fada masu.

Kungiyar ta gayyaci magoya bayan ta da su ci gaba da kai hare hare babu kakkabtawa, ga Amurika, a ko inna, kuma a ko wane lokaci.

A dazu nan ne a ka kawo karshen matakin farko, na zaben yan majalisun dokokin da a ka gudanar yau.

Zaben ya shafi yan malati, da wanda ke tsare kurku, da kuma jami´an tsaro.

A baki daya,yan majalisar dokoki 275 ne, za a zaba, da su zaman wa´adin shekaru 4, a majalisa.

Ranar alhamis ce, idan Allah ya kai mu, za a zaben gama gari, inda al´ummar kasa baki daya, zata kada kuri´a.

Saidai kamar yada a ka saba, kullum hare haren ta´adanci sun ci gaba da abkuwa ,inda a sahiyar yau ,sojoji Amurika 2 su ka bakunci lahira.

A dangane da wannan tashe tashen hankullla, kungiyar Gamayya turai,ta bayyana fasa tura wakilan ta, domin sa iddo ga zaben.