1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben yan majalisar Ukraine

Yau ne alummar kasar Ukraine ke kada kuriunsu domin zaban yan majalisar dokoki.Wannan na mai kasancewa zakaran gwajin dafin gwamnatin vicktor Yushenko masi sassauci,tun bayan hawan karagar mulkin wannan kasa a shekarata 2004.An dai bude rumfunan zabe a duk fadin kasar tun da karfe hudu na subahi,zaben da zai dauki tsawon saoi 15 yana gudana.Akwai kimanin jammiyun siyasa 45 dake takara a zaben yan majalisar dokokin Ukraine din.A yan watanni da suka gabata dai ,an samu koma baya a dangane da goyon bayan da jammiyar Yushenko ke samu ,sai dai akwai hasashen cewa tsohon premiern kasar Viktor Yanukovych,zai sake komowa fagen siyasa,inda ake saran jammiyarsa ce zata fi samun yawan kuriu a zaben yan majalisar na yau.