1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben ´yan majalisar dokokin kasar Botswana

Mohammad Nasiru AwalNovember 1, 2004
https://p.dw.com/p/Bvez
Tutar kasar Botswana
Tutar kasar Botswana

Sakamakon zaben da aka bayar yau litinin ya yi nuni da cewa jam´iyar Botswana Democratic Party, BDP ta shugaba Festus Mogae wadda ta lashe dukkan zabukan da aka gudanar a kasar tun bayan da Botsawana ta samu ´yancinta a shekarar 1966, ta samu kujeru 38 daga cikin 50 da aka ba da samakonsu. Yayin da babbar jam´iyar adawa ta Botswana National Front BNF ta ci kujeru 11 sannan ita kuma karamar jam´iyar Botswana Congress Party BCP a takaice ta samu kujera daya tak, wato jumullar kujeru 12 idan aka kwatanta da kujeru 7 da ´yan adawa suke da su a tsohuwar majalisar dokoki.

To amma masu lura da al´amuran da ka je su komo sun yi hasashen cewa ´yan adawa zasu samu kujeru 15 zuwa 20 daga cikin kujeru 57 na majalisar dokokin da aka yi takara kansu. An jiyo wani jami´in diplomasiyar yamma na cewa ko da yake an samu dan ci-gaba amma bai kai yadda suka yi tsammani ba.

Watakila da yawan kujerun da ´yan adawa suka samu ya fi haka, in da jam´iyar BCP ta shiga cikin kawance jam´iyun adawa karkashin jagorancin jam´iyar BNF. An bayyana cewa an kamanta adalci a wannan zabe. Amma masu lura da al´amuran yau da kullum sun ce jam´iyar BDP ta shugaba Mogae ka iya fuskantar matsaloli idan wasu ´ya´yanta suka juya mata baya a game da wasu batutuwa da suka shafi raba madafun iko.

A ran asabar da ta wuce shugaba Mogae yayi barazanar rusa majalisar dokoki idan ta yi kokarin hana a sake nada Ian Khama a mukamin mataimakin shugaban kasa. Ana kyautata zaton cewa Ian Khama wanda shine tsohon kwamandan askawaran kasar kuma dan shugaban kasar na farko Seretse Khama, shine zai gaji shugaba Mogae. Masu sukar lamirinsa na zarginsa da matsancin ra´ayi irin na mulkin kama karya. Bisa ga tsarin mulkin Botswana dai majalisar dokoki ce ke zaban shugaban kasa, kuma a gobe talata idan Allah Ya kaimu za´a yi bikin rantsad da Mogae wanda tsohon ma´aikacin asusun ba da lamuni na duniya ne, don yin tazarce a karo na biyu a birnin Gaborone. Duk da arzikin lu´ulu´u da Allah Ya huwace mata Botswana mai yawan al´uma miliyan 1.7 tana daya daga cikin kasashen nahiyar Afirka da ke fama matsalolin tattalin arziki da na marasa aikin yi. Hakazailka alkalumman da MDD ta bayar sun ce Botswana ta fi ko-wace kasa a duniya yawan masu kamuwa da kwayoyin HIV dake haddasa cutar AIDS ko kuma SIDA. Amma ana yabawa gwamnati bisa sahihan matakan da take dauka na yaki da yaduwar cutar.