1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben yan majalisar dokoki a Iraki

Zainab A MohammedDecember 15, 2005
https://p.dw.com/p/Bu3O
Hoto: AP

Kimanin yan Iraki million 15 ke kada kuriunsu ayau,a zaben yan majalisar dokoki dazai samarwa kasar cikakkiyar gwamnatin democradiyya tun bayan kifar da mulkin Sadam Hussein.

Rahotanni daga kasar Irakin na nuni dacewa akasarin wadanda suka cancanci kada kuriun nasu sunyi dafifi zuwa rumfunan zabe,musamman a garuruwa da yankun dake da mafi yawan yan darikar Sunni,wadanda sukayi watsi da zaben watan janairun daya gabata,batu da a daya hannun ke dadawa Amurka wadda ke fatan cewa wannan zabe zai kawo zaman lafiya,domin bata daman janye dakarunta daga cikin kasar ta Iraki.

To sai dai adauidai lokacin da aka fara bude rumfunan zaben da safiyar yau ,an barkewar sabbin hare haren rokoki a sassa daban daban na birnin Bagaza,da suka hadar da yankin nan dake dauke da gidajen manyan jamian gwamnati dana ketare da ake kira Green Zone.

Wani Dan kasar Irakin ya gamu da ajalinsa alokacin da tarwatsewar wata bomb a kusa da wani runfan zabe ya ritsa dashi,a garin Tal Afar dake arewacin kasar,kana wani mai tsaron asibiti ya rasa ransa a ,ayayin tashin wani bomb a kusa da rumfunan zabe a garin Mosul.

To sai sanin yadda kasar ta iraki da kewaye ke fama da barazanar hare hare da tashe tashen hankula,akwai alamun cewa an samu lafawa,kana sauran yankunan da aka fuskanci ire iren wadannan tashe tsahen boma bomai,yan Irakin sun yi jerin gwano zuwa cibiyoyin zaben domin kada kuriunsu ba tare da bayyana fargaba ba.

Wasu daga cikin yan Irakin da suka fita domin zaben yan majalisasr dokokin kasar dai na dauke da tutar kasar.

A birnin Bagadaza dai yan darikar sunni dake yankin Aadhamiya,inda kuma ake zargin cewa mafakace way an takifen kasar,wadanda akayi hira dasu sun bayyana cewa suna fatar samun gurbi domin tofa albarkacin bakin cikin harkokin gwamnati,wanda suka rasa tun kifar da Sadam Hussein.

A garin Mosul dake zama birni na Uku mafi girma a Iraki,Irakawan sunyi dafifi zuwa cibibiyoyin zabe ,duk da barazanar hare hare da aka kai a kusa wasu runfunan zabe tun da safe.

To sai dai a garin Kirkut dake da gamin gambizan larabawada kurdawa da turkawa,akasarin kabilan uku na kokarin bayyana cewa kowanensu ne keda rinjaye,ta hanyar kada kuriu mafi yawa.

Kurdawa kamar guda hamsin cikin kayan gargajiya dauke da furanni sukayi layi a wata cibiyar zabe.

Bugu da gari a garuruwan day an darikar Shia sukafi rinjaye kamar Kerbala da Najaf,mutane na fatan cewa wannan wata damace wa Iraki na samarwa kanta makoma na gari.

A garin Basra dake kudancin kasar kuma mafi girma na biyu a Irakin,Shiawa day an UIC dake da rinjaye sun bayyana muradinsu na marawa tsohon Prime minister Iyad Alawi baya..Kana a Falluja da aka fuskanci gwagwarmaya da yan ta kife,an samu karancin takardun zabe saboda yawan mutane da suka fito domin kada kuriunsu.

Jamiin zabe dake kula da cibiyar zabe ta Osama bin Zaid dake Falluja Abbas Mahmud,ya koka dacewa mutanen da suka fito kada kuriunsu sun zarce yawan takardun zabe da aka kebewa yankin.Bugu da kari jamming hukumar zaben Iraki Najib Mahmoud yace akwai mutane masu yawan gasket dake jerin gwano domin yin zabe,amma takardun zaben sun kare,wanda ya tilasta su naman haryar daukan jamaa zuwa wasu cibiyoyin zaben.

Garin Ramadi nacigaba da kasancewa daya daga cikin garuruwa dake fama da barazanar tashe tashen hankula a IRaki,inda ko da safiyar yau an fuskanci tashe tashen boma bomai adai lokacin da jamaa suka fara kada kuriunsu.Sai daui jamiin zabe dake kula da gunduwar Anbar wanda ya hadar da Ramadi,yace cibiyoyin zabe 162 daga cikin 207 ne aka bude ayau.

To sai dai ana kyautata zaton cewa jammiyar hadin gwiwa ta yan darikar shian Irakin ne zasu samu kujeru masu rinjaye a zaben nayau,amma bazai kaisu ga kafa gwammnati ba tare da hadin gwiwan wasu jammiyun adawa ba.Batu da manazarta ke ganin cewa zai dauki lokaci mai tsawo na mahawarar kafa zaunanniyar gwamnati a wannan kasa.Kimanin Irakawa million 15 nedai ke kada kuriunsu domin zaben yan majalisu 275,a karo na farko tun bayan kifar da gwamnatin Sadam Hussein.