Zaben ′yan majalisar dokoki a Cote d′Ivoir | Labarai | DW | 18.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben 'yan majalisar dokoki a Cote d'Ivoir

A wannan Lahadin ne 'yan kasar Cote d'Ivoir fiye da miliyan shida ke zaben 'yan majalisun dokokin kasar 255. Da misalin karfe takwas ne dai agogon GMT aka buda runfunan zabe 19,800 a kasar.

Wannan zabe na a zaman na farko a karkashin sabuwar jamhuriya ta uku bayan zaben rabagardama da ya amince da sabon kundin tsarin mulkin kasar a watan Oktoban da ya gabata. A cewar hukumar zaben kasar ta CEI, za a rufe runfunan zaben ne da misalin karfe shida na yamma agogon GMT, sannan kuma sakamakon zaben zai iya kai wa ranar Laraba kafin a same shi, sai dai kuma ana iya samun sakamakon wuccin gadi kafin wannan rana.

Duk da ana cewa mata za su taka rawar gani a fagen siyasar kasar ta Cote d'Ivoir, amma kungiyar mata da ke fafutikar samun daidaito tsakanin maza da mata a kasar, na ganin cewa babu takarar mata da yawa a zaben, inda ta ce mata 43 ne kawai daga cikin 'yan takara 1,337 ke yin takarar.