Zaben ´yan majalisar dattijan Zimbabwe | Labarai | DW | 26.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben ´yan majalisar dattijan Zimbabwe

A yau al´umar kasar Zimbabwe ke kada kuri´a a zaben ´yan majalisar dattawar kasar. To sai dai ana ganin zaben tamkar wani wasan yara wanda ke da nufin karfafa ikon da jam´iyar shugaba Robert Mugabe ke da shi akan ´yan majalisun dokokin kasar. Masu sa ido a zabe sun yi hasashen cewa mutane ba zasu fita sosai don kada kuri´a ba musamman a daidai lokacin da ake kara saka ayar tambaya dangane da rawar da wannan majalisa mai wakilai 66 zata taka. Zaben ya kuma janyo rarrabuwar kawuna a tsakanin jam´iyar adawa ta MDC game da kauracewa zabe ko a´a.