Zaben yan majalisa a Kuwaiti | Labarai | DW | 29.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben yan majalisa a Kuwaiti

Ayau ne alummar kasar kuwaiti ke kada kuriunsu domin zaben yan majalisar dokoki,inda a karon farko a wannan kasa ta larabawa mata ke samun daman takara,da kuma kada kuriunsu.A watan mayun 2005 nedai ,majalisar kuwaitin ta zartar da doka dake bawa matan kasar yancin yin takara da kuma kada kuriunsu ,a zaben wakilai 50 na majalisa,a wannan kasa dake da albarkatun man petur.

Jamian zaben kasar dai sun sanar dacewa akwai yan takara 250 dake neman haye kujeru 50 din,daga cikinsu kuwa akwai mata 28,wadanda suka lashi takobin samun nasara,duk da cewa yawancin maza yan takaran fitattun yan siyasa ne.

Dumbin alummar kuwaitin dai sunyi dafifi a cibiyoyin zabe ,inda maza ke kada kuriunsu daban da inda mata suke nasu jerin gwano,a wannan kasa ta musulunci.

Prime minista Sheikh Nasser al-mohammed al-sabah,ya bayyana cewa fitowar mata domin kada kuriunsu nasu,ya dada bayyana yadda kuwaiti ta marabci democradiyya da hannu biyu biyu.