1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben 'yan majalisa a kasar Bama

Gazali Abdou TasawaNovember 8, 2015

Miliyoyin mutane na kada kuri'ar zaben 'yan majalissar dokoki a wannan Lahadi, da ke zama na farkon irinsa a karkashin tsarin demokradiyya a shekaru 25 na baya-bayan nan

https://p.dw.com/p/1H1nb
Nachwahlen in Birma 2012
Hoto: dapd

Yanzu haka dai hankalin duniya ya karkata a kan fitacciyar 'yar adawar kasar shugabar jami'iyyar LND ta Ligue Nationale pour la Democratie wato Aung San Suu Kyi 'yar shekaru 70 a duniya wacce tun da sanhin safiyar wannan rana ta kada kuri'arta a wata runfar zabe da ke tsakiyar birnin Rangoun a gaban tarin 'yan jarida na duniya.

Daruruwan magoya bayan madugar 'yan adawar kasar ta Bama sun yi ta rera kalamai na nasara a lokacin da za ta kada kuri'ar tata. Ana kyautata zaton dai jam'iyyarta ta LND ta Aung San Suu Kyi ce za ta lashe zaben da zai bata damar karbar milkin kasar bayan da ta share gwamman shekaru tana fuskantar muzgunawa daga hannun milkin kama karya na sojojin kasar