Zaben ′yan majalisa a Indiya | Siyasa | DW | 20.04.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zaben 'yan majalisa a Indiya

Kimanin 'yan kasar Indiya miliyan dari shida da saba'in ne ke da 'yancin kada kuri'unsu a zaben majalisar dokokin kasar da aka fara a yau talata

Masu kada kuri'a a zaben Indiya

Masu kada kuri'a a zaben Indiya

Zaben yan majalisar dokoki na Indian dai na mai zama mafi girma da aka tabayi a tsakanin kasashen duniya,inda Jammiyar Hindu Nationalist mai mulkin kasar ke fatan amfani da harkokin inganta tattalin arzikin kasar wajen lashe zaben da akalla mutane million 670 ke kada kuriunsu.

Yau dindai Millioyoyin yan kasar ne sukayi jerin gwano a mazabu 140,wanda ke zama rukuni na farko daga cikin rukunoni 5 da zaayi ana gudanar da wannan zabe,wanda kuma ake saran sanar da sakamakonsa ranar 13 ga watan mayu ,idan mai duka ya kaimu.Bisa dukkan alamu daijammiyar prime minista Atal Behari Vajpayee,itace zata sake lashe mafi yawan kujeru daga cikin mazabu 545 da akeawa takara a majalisar dokin kasar,wanda bazai kasa nasaba da matakan data dauka na habaka tattalin arzikin Indian ba.Shugaban gwamnatin Indias dai yayi namijin kokari watanni biyar gabannin wannan zabe,wajen ganin cewa ya farfado da harkokin tattali,wanda kuma a hannu guda ya bawa jammiyarsa nasara a zaben shiyyoyi daya gudana a watan Disamban daya gabata.

To sai dai jammiyar adawa,a karkashin jagorancin Nehru-Gandhi dynasti,ta bayyana cewa ingantuwa da aka samu da wajen kashi 8 daga cikin 100 na tattalin arzikin kasar a shekarar data gabata,na daga madaukakin sarki ne amma ba Jammiyar BJP mai mulki ba,kamar yadda take ikirari.Jammiyar adawar dai ta misalta cewa,sakamakon hali na kunci da talauchi da kasar ke ciki,ya haddasa mutuwan mata 20 da kananan yara 2,a ranar 12 ga watan Aprilu,sakamakon cunkoso a wajen liyafar campaign manajan Vajpayee,Lalji Tandon.Yini biyu kafin wannan zaben dai,Tandon ya sanar dayin murabus daga mukamin nasa,domin gudun batawa Prime minista Suna da daman yin nasara.Vajpayee,mai shekaru 79 da haihuwa,ya kasance mafi fitaccen dan siyasa idanun alummar ta India.

Masharhanta dai sun bayyana cewa babu alamun akwai wata jammiyar adawa da zata kusanci mai mulkin da yawan kujeru a wannan zabe da aka fara yau.A tsohuwar majalisar Indian dai,kimanin jammiiyyu 43 suka samu wakilci.

Bayan kada kuriarsa ayau a jihar Gujarat dake yammacin India,mataimakin prime minista Lal Krishna Advani,ya bayyana cewa koda jammiyar BJP ta samu rinjaye a majalaisar,gwamnatin hadin gwiwa zaa nada ,kamar yadda suka sha nunarwa a baya.

Zaben wannan kasa dake zama karo na 14 kenan bayan zamun yancin kai,kana na hudu tun daga shekara ta 1996,na mai zama na farkon irinsa da ake amfani da naura mai aiki da lantarki ,domin kare zargin da ake yawaitayi na magudi.To sai dai jamian zabe na dogaro ne da amfani da Giwaye,da dawakai da kananan jiragen ruwa ,wajen daukan wadannan naurori zuwa yankunan karkara da ababan hawa basa iya zuwa,ayayinda wakilan jamiiyu ke taimakawa kauyawan banbanta jammiiyun ta hanyar manna alamu a kirjinsu.

Ana dai sanin sakamakon zaben na India ne gabannin kareshi,musamman dayake akasarinsa na dogaro ne kann banbancin kabilanci,sai dai BJP na amfani da siyasar ta na ketare wajen ganin cewa ta samu nasara,musamman ma dangantaka daya ingantu tsakanin India da Pakistan ,wanda har shugaban gwamnatin na India ya kai ziyara kasar Pakistan,da kuma sakarwa harkokin kasuwanci mara,wanda ya jagoranci ingantuwan tattalin arzikin kasar a shekarar data gabata.

A yau dindai kimanin mutane million 35 daga cikin million 175,suka kada kuriun nasu a saoi 10 na farko.Sai dai jaminan yansandan kasar sun sanar dacewa akalla mutane 16 suka rasa rayukansu a rikici rikice dake da nasaba da zabe,akasarinsu kuwa a Kashmir.A yankin kashmir da Bihar da Jharkhand kadai,hukumar zaben ta ware cibiyoyin zabe kimanin dubu 66,ayayinda aka tura jamian yansanda dubu 117,domin tabbatar da tsaron rayukan jamaa.