1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben yan majalisa a Afganistan

Zainab A MohammadSeptember 19, 2005

Kashi 50 daga 100 na yan kasar sun kada kuriunsu

https://p.dw.com/p/BvZZ
Hoto: dpa-Bildfunk

Jamian kasashen duniya masu gani da ido sun yabawa yadda zaben yan majalisun kananan hukumomi ya gudana a jiya lahadi a Afganistan,batu dake bayyana alamun nasara,sai akwai rahitanni dake nuni dacewa mutane million 6 kachal suka kada kuriunsu,wanda ke nunfin kashi 50 daga cikin 100 na yawan wadanda suka cancanci zabe.

Jamian zabe da masu gani da ido daga kasashen waje sunyi bayanin cewa,jamaa dayawa basu fito domin kada kuriunsu ba,idan aka kwatanta da hasashe da akayi tun da farko na cewa mutane zasuyi dafifi zuwa cibiyoyin zabe,batu da bazai kasa nasaba da matsalolin barazana na rashin tsaro ba.

Shugaba Hamid Karzai na Afganistan din dai ya yabawa alummar kasar da suka samu sukunin fitowa domin shiga harkokin zabe duk da barazana da yan ta kife sukayi na afkawa wuraren zabe.

Wannan dai na mai kasancewa wata babbar nasara ce a yunkurin da akeyi na farfado da Democradiyya a wannan kasa wanda ke bisa tsarin sake ginin kasar bayan rusa gwamnatin yan taliban da Amurka tayiwa jagoranci a shekara ta 2001.

Jakadan Amurka A Afganistan Ronald Neumann ya fadawa taron manema labaru a birnin kabul cewa,dole ne ayabawa alummar kasar saboda wannan rawa da suka taka a karo na farko cikin shekaru 30 da suka gabata,na zaban yan majalisun dokoki da zasu wakilcesu.

A yanzu haka dai Amurkan nada dakarunta kimanin dubu 20,dake yakan yan rusasshiyar gwamnatin taliban.Mr Neumann yace duk dacewa an fuskanci mace mace ,baa fuskanci tashe tashen hankula ba lokacin zaben na jiya.Koda yake injishi da sauran rina a kaba,musamman wajen ingantuwan harkokin sharia ,da sashin tsaro ,wadanda sune batutuwa biyu da zasu zamanto kalubale wa shugaba Hamid Karzai da wadannan yan majalisu nasa da aka zaba jiya.

Shima jakadan kungiyar gamayyar turai a wajen zaben, Emma Bonino ,ya yabawa wannan kyakkyawan mataki na cigaba da democradiyya ta samu a Afganistan.

Bisa ga rahotannin dake fitowa daga sassa daban daban na kasar dai,kashi 50 daga cikin dari na wadanda suka cancanci zabe ne suka kada kurun nasu a zaben na jiya.

Mayakan rusasshiyar gwamnatin Taliban dai sunyi gargidi wa alummar kasar kan su kauracewa zaben na jiya lahadi a wannan kasa da har yanzu ke cikin hali na tsaka mai wuya dangane da harkokin tsaro.

Shugaban hukumar zabe na afganistan Peter Erben ya fadawa taron manema labaru cewa ,yawan wadanda suka kada kuriun nasu a jiya sun gaza na wadanda suka kada kuriu a zaben shugaban kasa.Sai dai yace dayake baa kammala tattara sakamako ba,wata kila zuwa karshe yawansu zai zarce na yanzu.Ana dai cigaba da karban sakamakon zaben.