1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben shugabanni a wasu kasashen Afirka

August 3, 2017

A cikin watan jiya na Yuli da kuma na Agusta da ake ciki, hankalin duniya ya kasance kan kasashen Senegal da Kenya da kuma Ruwanda, sakamakon zaben jagororin manyan mukaman da za su tafiyar da kasashen na wasu shekaru.

https://p.dw.com/p/2hdsj
Wahlen Senegal 2012
Hoto: Reuters

Ana sa ran samun sauyi a matakan shugabancin kasashen Senegal da Kenya da kuma Burundi. A kasar Senegal dai kawancen jam'iyyu masu goyon bayan Shugaba Macky Sall ne suka lashe zaben 'yan majalisa da aka yi a kasar. Kasashen Burundi da Kenya kuwa, za su yi zaben shugaban kasa ne a ranakun da ke tafe. Ruwanda za ta yi zabenta ne a ranar Juma'a 4 ga watan Agusta, yayin da ita kuwa da Kenya za ta zabi nata shugaban a ranar Talata 8 ga watan na Agusta.

Masana da 'yan kasa sun yi sharhi kan wadannan zabuka da akasari ake ganin jijiyoyin wuya sun tashi. 

Tsallake zuwa bangare na gaba Rahotanni da Sharhuna

Rahotanni da Sharhuna