1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya ya jawo sabuwar dambarwa a siyasar kasar

May 27, 2013

PDP ta dakatar da gwamnan jihar Rivers abin da ke nuna kara dagulewar rigingimun da su ka biyo bayan sake zabensa a matsayin shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya.

https://p.dw.com/p/18f7e
©Jonathan Rebboah/Wostok Press/Maxppp France, Paris 25/11/2011 Le president du Nigeria Goodluck Jonathan arrive au palais de l Elysee The President of Nigeria Goodluck Jonathan at the Elysee Palace
Goodluck JonathanHoto: picture alliance / dpa

Darewa gida biyu da Kungiyar gwamnonin Najeriya ta yi tun bayan zaben shugaban kungiyar da ya haifar da takkaddama mai zafi, inda bangarorin biyu na gwamnan jihar Rivers Rotimi Amaechi da aka sanar da zabensa a matsayin wanda ya lashe zaben da na gwamnan jihar Pilato Jonah Jang da ke jan daga a matsayin shine shugaban Kungiyar na ci-gaba da kalubalantar hadewar kungiyar ta gwamnonin Najeriya da a baya ake ganin ta a matsayin tsintsiya madaurinki daya.

Duk da nisanta kanta da fadar shugaban Najeriya ta dade tana yi da wannan rikici, saboda sanin takkaddamar da gwamnan jihar Rivers din yake fuskanta da shugaban Najeriyar, to sai dai sanar da dakatar da gwamnan jihar Rivers din daga jam'iyyar PDP mai mulki a Litinin din nan ya kara nuna a fili dagewar da gwamnonin 18 da ke goyon bayan gwamnati ke yi na dandanawa gwamnan kudarsa a jam'iyyar da ma dagulewar wannan rikici da masahrahanta ke nuna yadda ya ke naso da ma shafar zaben 2015 da tuni guguwarsa ke kadawa.

Tuni dai gwamnan na jihar Rivers Rotimi Amaechi ya maida murtani a kan korar tasa daga jam'iyyar da ya danganta da koken da reshen jam'iyyar na jihar ya gabatar yana mai cewa

Rabiu Musa Kwankwaso, Gouverneur von Kano. Thomas Mösch, 9.5.2013, Kano/Nigeria. Rabiu Musa Kwankwaso, Gouverneur von Kano State (Nigeria) seit 2011 (bis 2015) und zuvor von 1999 bis 2003.
Rabiu Musa Kwankwaso Gwamnan KanoHoto: DW/T. Mösch

‘'Yace: dole ne jam'iyyata ta mike tsaye don watsi da siyasa irin ta yarfe da tursasawa, batun da suke na karamar hukumar Obiyabor ba gwamna ne ya dakatar da shugabanin karamar hukumar ba, duk da cewa ina da ikon yin haka, amma ban kaiga yin hakan ba. Ban sani ko a matsayina na gwamna don kawai na mike ina neman 'yancina sai a ce na ci amanar jam'iyya?''

Irin yadda wannan zaben kungiyar gwamnonin Najeriya da bisa ka'ida bai kamata ya dauki hankali har ma da zafafa fagen siyasar kasar ba, da a yanzu yake nuna tankara ana kada kugen zaben 2015 din ne ya sanya Dr Sadeeq Abba masanin kimiyar siyasa da ke jami'ar Abuja bayyana cewa akwai abinda wannan ke nunawa da ya kamata a yi la'akari da shi.

A yayin da gwamnan jihar Filato Jonah Jang ke ci gaba da jan daga a kan lallai shine zababben shugaban kungiyar gwamnonin Najeriyar bisa tsarin karba-karba da ya kamata shugabancin kungiyar ya koma arewacin Najeriyar da gwamnonin 18 ke goya masa baya na kara jefa rudani a kan wannan batu.

To sai dai ga Gwamman jihar Rivers yana mai nuna mamaki a kan wannan lamari musamman a cewarsa yadda aka gudanar da zabensa da aka kasa a faifai da ya bashi ikon samun rinjaye.

Yace idan mu gwamnonin 36 muka yi zabe bisa tsarin kada kuri'a a sirce muka fitar da sakamako shin me zai hana mu amince da sakamakon. Idan har mu shugabanin Najeriya wato gwamnonin muka ki amincewa da zaben da aka shirya shi sosai, sai kawai wani yace a'a akwai wata takarda da muka sa hannu a watan Afirlu amma sai 24 ga watan Mayu ya kawo wannan takardar bayan mun gama zabe, shin wane irin magudin zabe ne wannan? Ba wai abu mai muhimmanci ba ne cewa ni Ameachi na ci zabe ko na fadi, abu mai muhimmanci shine in har muna konkanto da ma jayaya a kan sakamakon irin wannan shin me zai faru a 2015?

Kashim Shettima, Gouverneur von Borno State, Nigeria Usman Shehu, 15.06.2011, Maiduguri / Nigeria
Kashim Shettima, Gwamnan BornoHoto: DW

Abin da zai faru kam shine ke daukan hankalin alummar Najeriyar da ma zafafa siyasar kasar, musamman yadda za ta kaya tsakanin bangarori biyu da suka ja daga da ma jam'iyyar PDP da a yanzu za'a sa idon ganin mataki na gaba da kwamitin ladabtarwa za ya dauka akan gwamnan na jihar Rivers a wannan sarkaniyar da ta ke tasirin ga siyasar Najeriya.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Yahouza Sadissou Madobi