1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben shugaban kasar Burkina Faso a yau lahadi

November 13, 2005
https://p.dw.com/p/BvLO

A yau ake gudanar da zaben shugaban kasa a Burkina Faso inda bisa ga dukkan alamu shugaba mai ci wato Blaise Compaore zai samu nasarar yin ta-zarce. To sai dai ´yan adawa wadanda suka yi alkawarin inganta harkokin ilimi da kiwon lafiya da rage yawan marasa aikin yi, sun zargi shugaban da yin amfani da dukiyar kasar a hanyoyin da ba su dace ba musamman wajen yakin neman zabe. Majiyoyin ´yan diplomasiyar kasashen yamma sun ce lalle shugaba Compaore yayi amfani dukiyar kasar da kuma kudaden da ya samu daga abokannensa shugabannin wasu kasashen waje a yakin neman zabe. Batun tsaro ya zama jigo a yakin neman zaben musamman saboda fashi da makami da ya zama ruwan dare a manyan hanyoyin kasar. Tun a cikin shekara 1987 Compaore ya dare kan kujerar shugaban kasar bayan wani juyin mulkin da ya kifar da shugaba Thomas Sankara.