Zaben shugaban kasa da na yan majalisa a kasar Tanzania | Labarai | DW | 14.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben shugaban kasa da na yan majalisa a kasar Tanzania

A kasar Tanzania yau ne a ke zaben shugaban kasa, gami da na yan majalisun dokoki, da na Kansiloli.

Tun shekara ta 1992, da kasar ta koma bisa turbar Demkradiya, wannan shine karo na 3, da a ka shirya zaben gama gari.

A kalla, mutane million 16, ya cencenta su kada kuri´u.

Daga jerin yan takara 10, dake neman maye gurbin shugaba Benjamin Mkappa, masu kula da harakokin siyasa a kasar, na hasashen cewa, dan takara jami´yar da ke rike da ragamar mulki,wato Jakaya Kikwete, zai taka mahimiyar rawa.

Shugaba mai ci yanzu, Benjamin MKapa, kamar yada tsarin dokokin kasa su ka tanada, ba shi cikin yan takara.

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, ya shaida wa manema labarai cewa, zaben na wakana lau lami.

A bangaren zaben yan majalisun dokoki, jam´iyu 17 su ka jera yan takara, domin zaben yan majalisu 232.

A rufe runfunan zabe dazun nan, saidai, an fuskanci yan matsaloli nan da cen , mussamman a tibirin Zanzibar, inda jami´an tsaro su ka harbi sama, domin tarwatsa matasa, masu goyan bayan jam´iyun adawa, da su ka bukaci kora wasu mutane, da ke bukatar zabe, tare da zargin cewa ba yan mazabar bane.