Zaben Shugaban kasa a Turkiya | Labarai | DW | 21.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben Shugaban kasa a Turkiya

Ministan harkokin wajen kasar Turkiya Abdullah Gul ya gaza samun nasara a zagayen farko na kuriun da yan majalisar dokokin kasar suka kada don zabansa a matsayin shugaban kasar na farko mai tsatstsauran raayi na musulunci.Ya samu kuriu da da dama amma ya gaza samun kashi biyu bisa uku da ake bukata.A watan Afrilun da ya gabata sai da masu goyon bayan raayi na walwalan addini da sojojin kasar su ka zama karan tsaye ga yunkurin Gul na zama shugaban kasar.Hakan ne ya kai ga gudanar da zaben gama gari da ya harzuka jamiyar AK ta prime ministan Recep Tayyip Erdogan a watan Yulin da ya gabata.Jamiyar adawa ta Republikan ta kauracewa zaben da aka gudanar jiya litini.Wakilanmu sun nunar da cewa Gul sai samu ribnjaye a zaben zagaye na uku da za a gudanar a mako mai zuwa.