Zaben shugaban kasa a Tajikistan
November 6, 2006Talla
Alummomin kasar Tajikistan nacigaba da yin dafifi zuwa cibiyoyin zabe domin kada kuriunsu a zaben shugaban kasa,zaben da ake ganin cewa Shugaba Emomali Rakhmonov na yanzu ,zai sake samun nasarar komawa madafan iko.Rahotanni daga kasar dai na nuni dacewa sama da kashi 65 daga cikin 100,na masu zaben kasar sun rigaya sun kada kuriun su,a saoi shida na farkon ranar zaben na yau.To sai dai tuni shugaba Rakhmonov yayi watsi da kalaman sukan daga masu gani da ido na kasashen turai ,akan tsarin yadda zaben ke gudana.Ya hakikance cewa zaben na gudana ne bisa tafarkin Democradiyya,sai dai ya gaza tsarin na kasashen turan.