1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

zaben shugaban kasa a Sri Lanka

November 17, 2005
https://p.dw.com/p/BvKl

A kasar Sri lanka an fara zaben shugaban kasa a ranar yau alhamis.

A na gudanar da wannan zabe ,cikin yanayin mattakan tsaro mai kwari, a dalili da tashe tashen hankulan da su ka wakana jiya, a kudancin kasar da ke fama da rikicin tawaye wanda su ka yi sanadiyar mutuwar 6.

A kalla mutane millions 13 ne, ya cencenta su ka kada kuri´u domin fida gwani daga jerin yan takara 13, da su ka shiga gwagwarmayar maye gurbin shugaba mai barin gado Shandrika Kumaratunga, da ke bisa karagar mulki tun 1994.

A jimilce runfunan zabe 10 da dari 5 sun fara aiki tun karfe 1 agogon GMT za su kuma rufe a karfe 10.

Kakakin hukumar zabe ya bayana wa manema labarai cewa, ya zuwa yanzu zabwen na wakana lau lami.

A lokacin yakin neman zabe, yan takara 2 da a ke sa ran, za su zo sahun gaba, sun bayyana manufofi da su ka sha banbam da juna, a game da batun warware rikici tawayen yan Tamul a wannan kasa.

Rundunar tawayen ta Tamul, ta sanar cewa ba zata nuna goyan baya ba, ga ko daya daga yan takara.