Zaben shugaban kasa a Portugal | Labarai | DW | 22.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben shugaban kasa a Portugal

A yau al´umar Portugal ke kada kuri´a a zaben sabon shugaban kasar. Kuri´ar jin ra´ayin jama´a da aka gudanar ta nuna cewa tsohon FM mai sassaucin ra´ayin ´yan mazan jiya Anibal Cavaco Silva ke gaba a kan sauran ´yan takara na masu ra´ayin sauyi. Masu kalubalantarsa dai sun hada da dan majalisa mai ra´ayin gurguzu Manuel Alegre wanda ke takara a matsayin indipanda sai kuma tsohon shugaban kasa Mario Soares. Idan ba´a samu dan takarar da ya samu fiye da kashi 50 cikin 100 na yawan kuri´un da aka kada ba, to za´a gudanar da zagaye na biyu tsakanin mutane biyu da suka fi samun yawan kuri´u a ranar 12 ga watan fabrairu.