Zaben shugaban kasa a Nigeria | Labarai | DW | 21.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben shugaban kasa a Nigeria

An fara rufe runfunan zabe,bayan kada kuriu a zaben shugaban kasa dana yan majalisar tarayya a NigeriaA jihar kano dake yankin araewacin Nigeriayar dai yan jarida sun ruwaito cewa baa fara gudanar da zaben akan lokaci ba,ayayinda wasu da sukayi jinkirin zuwa aka hanasu kada nasu kuriun.Akasarin cibiyoyin zaben dake fadin tarayyar Nigeriar dai sun rufe kafin lokacin da aka tsayar na rufewa,sakamakon karewan kayayyakin aikin zaben,kamar yadda jamian suka shaidar.Sai dai jamiai daga headquatar hukumar zabe dake birnin Abuja,sun ce komai dangane da wannan korafi.Sai dai an dage gudanar da zaben shugaban kasar dana yan majalisar tarayyar a wasu sassan Nigeria,sakamakon kura kurai da aka samu akan takardun gudanar da zaben.