Zaben shugaban kasa a Mali | Labarai | DW | 29.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben shugaban kasa a Mali

A Kasar Mali jamaá na cigaba da kada kuriá a zaben shugaban kasa wanda ke zama karo na hudu da kasar ke gudanar da zabe bisa tafarkin dimokradiya. Ko da yake kasar ta Mali na fama da talauci, ta kasance abar misali ta fuskar dimokradiya a Afrika. Daga cikin yan takara takwas dake fafatawa a zaben, jamaá da dama na hasashen cewa shugaba mai ci a yanzu Amadou Toumani Toure wanda ke da goyon bayan hadin gwiwar jamíyu 43 a karkashin inuwar Alliance for Democracy Party shi zai lashe zaben. Babban mai kalubalantar sa shine shugaban majalisar dokokin tarayya Ibrahim Boubakar Keita. Yan kasar Miliyan shida da dubu dari tara wadanda aka yiwa rajista ke kada kuriá a zaben na yau. Kasar Mali ita ce kasa ta uku masu arziki luú luú a nahiyar Afrika amma kuma ta kasance daga cikin kasashe matalauta na duniya.