1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben shugaban kasa a Kazachstan mai arzikin man fetir a tsakiyar Asiya

December 4, 2005
https://p.dw.com/p/BvI9

An fara kada kuri´a a zaben shugaban kasar Kasachstan dake tsakiyar nahiyar Asiya. Ana sa rai cewa shugaba mai ci Nursultan Nazarbayev zai yi nasara akan sauran ´yan takara biyar da suka tsaya a zaben. Tun a cikin shekarar 1990 shugaba Nazarbayev mai shekaru 65 da haihuwa yake shugabantar kasar mai arzikin man fetir. Tun a lokacin yakin neman zabe ´yan takara na bangaren ´yan adawa suka zargi hukumomin kasar da tursasa musu, yayin da kafofin yada labarun kasar suka ke ta yiwa shugaba Nazarbayev kamfen. Wakilan kungiyar tsaro da hadin kai a Turai wato OSCE ke kula da yadda zaben ke gudana. Kawo yanzu dai ba wani zabe da aka taba yi a kasar ta Kazachstan da ya dace da dokokin demokiradiya na kungiyar OSCE.