Zaben shugaban kasa a Gabon mai arzikin man fetir | Labarai | DW | 27.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben shugaban kasa a Gabon mai arzikin man fetir

A kasar Gabon ma a yau lahadi ake gudanar da zaben shugaban kasa, inda bisa ga dukkan alamu shugaba mai ci Omar Bongo zai lashe wannan zabe. Tun a shekarar 1967 shugaban mai shekaru 69 da haihuwa ya ke shugabantar kasar ta Gabon. Yanzu haka dai shine shugaban Afirka mafi dadewa akan karagar mulki. ´Yan adawa da suka yi zargin tabka magudi a zaben da aka yi a baya, a yanzu ma suna korafin cewa shugaban Bongo zai yi aringizo kuri´u don yayi tazarce a kan kujerar shugaban kasar mai arzikin man fetir.