Zaben Shugaban kasa a Cote divoire
November 28, 2010Yau al'uma ke kada kuriaa a zaben shugaban kasa zagaye na biyu a kasar Cote divoire.Mutane sama da miliyion biyar ne da aka yi regista ake san ran zasu jefa kuriaa a zaben dake ciki da tarihi ga kasar bayan shekaru 11 na rikicin siyasar da aka yi fama da shi.Yan takara biyu ne dai zasu kalubalanci juna , fitace shugaban Laurent gbagbo da tsofon fraministan alassane watara. A zagaye na farko laurent gbagbon shine ke kan gaba da kishi 38 cikin dari na kuriu da aka kada yayin da tsofon fraministan ke da kashi 32.zaben na gudana cikin tsatsaura matakan tsaro bayan zanga zangar da aka yi a jiya wacce ta yi sanadiyar mutuwar mutane ukku a sa'ilin da wasu magoya bayan Alassane Ouatara ke nuna rashin amincewarsu da kafa dokar hana fita dare da shugaban kasar ya yi
Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Abdullahi Tanko Bala