1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben shugaban kasa a Burkina Faso

Yahouza SadissouNovember 13, 2005

An kammala zabe shugaban kasa lau lami a Burkina Faso

https://p.dw.com/p/Bu4E

A Burkina Faso na cikin jiran sakamakon zaben shugban kasa zagaye na farko da ka gudanar jioya afadin kasar baki daya.

Mutane da dama sun halarci runfunan zabe, domin tantance gwani, daga jerin yan takara 12 da su ka hada da shugaba mai ci yanzu Blaize Kampaore.

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, Musa Mishel Tapsoba, ya sanar manema labarai cewa, zaben ya gudana lami lahia, a ko inna cikin kasa.

Saidai an fuskanci yan matsaloli da ba su taka kara ba sun karya, a wasu wurare, dalili da karancin takardun zabe ko kuma ketare wasu daga sunayen masu zaben.

Duk da cewa an fara kidayar kuri´u tun daren jiya shugaban hukumar zanen ya ce ba za su bada sakamako ba kafin 17 ga wata.

To bayan farfado da tsarin demokaradiya a kasar Burkina Faso, a shekara ta 1991,wannan shine karo na farko, da ka dama da yan adawa cikin harakokin zabe.

A zabbukan da su ka gudana a shekara ta 1991 da kuma 1998, kwata kwata sun kaurace, bayan sun zargi Blaize Kampaore da shirya magudi.

Shugaba Blaise, da ya share shekaru 18 bisa karagar mulki, ya bayana cewa a wanan karo ma, babu shakka, zai lashe zaben na jiya, ta la´akari da yadda jam´iyar sa, da sauran gungun jam´iyunnda su ka mara masa baya, ke da dimbin jama´a.

Baban mai adawa da shugaban kasa, wato Benewende Stanislas Sankara, ya kada kuri´ar sa, a ma´aifar tsofan shugaban kasar Burkina Faso Tomas sankara, don nuna karamci ga mirganyin da sunan sa, ya samu karbuwa a fagen siyasar Burkina Faso.

Masu kulla da harakokin siyasa a wannan kasa, sa sun tabbata,r da Blaize za shi tazarce, saboda rabuwar kanu da a ka samu tsakanin jam´iyun adawa, kasancewar sun kasa tsaida, dan takara daya, da za shi wakilce su a wannan zabe.

Yan kallo daga kasashe da kungiyoyi daban daban na dunia, su kimanin dubu daya, su ka sa iddo ga zaben, tare da jami´an tsaro dubu 24.

Ya zuwa rufe runfunan zaben, rahotanin da da dama daga cikin yan kallon su ka bayyana, na nuni da cewa an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali, da tsari, saidai yan matsaloli nan da cen da ba za a rasa ba.