Zaben shugaba kasa zagaye na biyu a Saleon | Labarai | DW | 08.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben shugaba kasa zagaye na biyu a Saleon

A yau ne alummomin kasar Saleon ke kada kuriunsu, azaben shugaban kasa zagaye na biyu ,sai dai yan takaran biyu sun koka dangane da musgunawa,wanda zai iya shafar kima da sahihancin wannan zabe.Mataimakin shugaban kasa mai barin gado kuma dan takara a wannan zabe,Solomon Berewa,ya zargi jamian yansanda da cin zarafin wakilan jamiiyyarsa masu sa ido,lokacin zaben na yau.Ayayinda ahannu guda kuma shugaban jammiiyyar adawa Ernest Koroma yace ,an hana wakilan jamiiyyarsa zuwa wasu cibiyoyin kada kuriun.A zagayen farko na zaben shugaban kasar ta Saleon,wanda aka gudanar kusan wata guda daya gabata,dukkannin yan takaran biyu sun gaza samun kashi 55 daga cikin 100,na yawan kuriu da ake bukata domin yin nasara.Koroma ya samu kashi 44 ,ayayinda Berewa ya samu kashi 38 daga cikin 100,A wannan zagaye dai,wanda ya samu mafi yawan kuriu,shine zai kasance shugaban kasa.