1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben Rasha 2024: Me ya sa Putin ya damu da yin zabe?

Abdourahamane Hassane
March 15, 2024

Duk da cewa Vladimir Putin ya hakikance zai ci nasara a zaben na 2024, yana so ya nuna tamkar yana dimukuradiyya a cewar masana.

https://p.dw.com/p/4dj3Z
Rumfar Zabe a Rasha
Hoto: Vitaly Timkiv/Sputnik/IMAGO

Al'umma a kasar Rasha na kada kuri'a a zaben shugaban kasa wanda kawai zai kara wa Vladimir Putin wa'adin shekaru shida na mulki. Zaben dai na zuwa ne bayan murkushe 'yan adawa, kuma ya biyo bayan mutuwar babban mai sukar lamirin Putin kuma dan adawar kasar Alexei Navalny. 

Shugaban Rasha Vladimir Putin
Hoto: Evgenia Novozhenina/REUTERS

Babu wata tantama Vladmir Putin, wanda ya shafe shekaru 25 yana jan ragamar mulkin kasar Rasha, zai lashe wa'adi na biyar a wannan zabe da ke gudana daga ranar 15 zuwa 17 ga watan Maris. Putin zai ci gaba da kasancewa a kan mulki har zuwa shekara ta 2030.

Kotunan Rasha ciki har da kotun koli sun haramta wa dan adawar da ya tilo a fili, dan siyasa mai sassaucin ra'ayi Boris Nadezhdin, tsayawa takara.

Sauran 'yan takarar sun hada da Nikolai Kharitonov, mai shekaru 75, wanda ke wakiltar jam'iyyar 'yan gurguzu. Dan takarar wannan jam'iyyar yawanci ya kan zo na biyu bayan Putin, duk da cewa na biyu ne mai nisa. Kharitonov ya soki wasu manufofin Putin na cikin gida amma yana goyon bayan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine.

Vladislav Davankov yana cikin 'yan takara mafi karancin shekaru. Yana da shekaru 40 ya gabatar da kansa a matsayin mai sassaucin ra'ayi. Sai dai kuma ya ce ba zai soki abokan hamayyarsa na siyasa ba.

A cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters, Kharitonov da Davankov kowannensu na iya samun tsakanin kashi hudu zuwa biyar cikin dari na yawan kuri'un da aka kada.

Sai dai duk da cewa masu sa ido na Rasha sun ce Putin na shirin yin nasara, amma a zahiri zaben shugaban kasar Rasha yana da wata manufa. Manufar ita ce ta magance kalubalen ciki da waje da gwamnatin Putin ke fuskanta, inji Konstantin Kalachev, mai sharhi kan harkokin siyasa kana tsohon mashawarci a fadar Kremlin.

Russland | Protest zur Unterstützung des inhaftierten Kremlkritikers Nawalny
Hoto: Kirill Kukhmar/TASS/dpa/picture alliance

"A waje, shi ne ya nuna cewa Putin, kamar madubi ne, yana aiwatar da manufofin da suka dogara da bukatun jama'a, wanda ke nuna cewa shugaban kasa da yawancin al ummar Rasha, gamayya ce guda ɗaya don kawar da duk wani ruɗani na kasashen yammacin duniya."

A cikin kasar, zaben na ba da damar halasta ikon shugaban kasa, ya nuna cewa al'ummar Rasha sun amince da ikon shugaban kasar. Ta bayan fage gwamnatin ta Rasha ta kaddamar da gagarumar kampe manufarta ita ce fitowar masu kada kuri'a da kashi 80 cikin dari. domin nuna wa duniya yadda zaben ya samu karbuwa ta hanyar zaburar da ma'aikatan gwamnati da manyan kamfanoni, masu biyayya ga gwamnati, da 'yan uwa da abokan arziki kowa ya fito ya kada kuri'a domin duniya ta ga cewa jama'ar Rashar na kaunar Putin.

Yawancin 'yan adawar Rasha dai sun fice daga kasar, amma sun yi kira ga magoya bayansu da su dauki mataki a lokacin zaben. Matar tsohon shugaban 'yan adawar  Alexei Navalny wanda ya rasu a baya-bayan nan, ta yi kira ga magoya bayanta da su fito rumfunan zabe baki daya da tsakar rana a ranar Lahadi 17 ga watan Maris domin karrama mijinta da ya rasu. Nikolay Petrov, mai ba da gudumawar bincike a cibiyar kula da tsaro ta Jamus ya kuma ce babu sauki ga Putin wajen gamuwa da adawa

"Kuskure ne a yi tunanin cewa ya fi sauƙi ga gwamnatoci masu iko su yi zaɓe sannan na dimokuradiyya. Ko mulkin kama karya ka ke yi akwai wadanda za su sadaukar da rayuwar su''

Yanzu haka dai rahotanni daga birnin Moscow na cewar zaben na Rasha ya fuskanci cikas na zanga-zanga da sabbin hare-hare daga Ukraine a yankunan kan iyaka. Yayin da aka kama wata mata bayan ta kona wata rumfar zabe a birnin Moscow, kamar yadda kafafen yada labaran Rasha suka rawaito.