1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben raba gardama a Turkiya

April 16, 2017

Batun ya raba kawunan jama'ar kasar inda masu goyon baya ke cewa sauyin zai karfafa zaman lafiya masu adawa kuma na cewa zai kai kasar Turkiya ga tafarki na mulkin kama karya.

https://p.dw.com/p/2bJfD
Türkei Referendum Wahllokal in Diyarbakir
Hoto: Getty Images/AFP/I. Akengin

Al'ummar Turkiya na kada kuri'a a zaben raba gardama domin amincewa ko akasin haka da shirin gyaran kundin tsarin mulki da zai sauya fasalin siyasar kasar da ma tsarin dimokradiyarta. Tuni dai batun ya raba kawunan jama'ar kasar inda masu goyon baya ke cewa sauyin zai karfafa zaman lafiya masu adawa kuma na cewa zai kai kasar ga tafarki na mulkin kama karya.

Mutane fiye da miliyan 55 ne ake sa ran za su kada kuri'unsu a mazabu dubu 167 a fadin kasar. Yayin da yan kasar kimanin miliyan uku wadanda ke zaune a kasashen ketare suka kada su kuri'unsu tun daga ranar 27 ga watan Maris zuwa 9 ga wannan watan na Aprilu a ofisoshin jakadancin Turkiyar da ke wadannan kasashe.

Türkei Referendum Wahllokal in Ankara Oppositionspolitiker Kemal Kilicdaroglu CHP
Kemal Kilicdaroglu jagoran 'yan adawa na Turkiya yana kada kuri'aHoto: picture-alliance/AP Photo/B. Ozbilici

An dai raba katin zaben ne gida biyu da ke nuna alamun E ko kuma A'a, ba tare da an rubuta wata tambaya ba, inda ake tsammanin jama'a sun san abin da suke so su zaba. An bude rumfunan zabe tun misalin karfe bakwai na safe za kuma a rufe karfe 4:00 na maraice. Sai dai za'a rufe rumfunan zabe a gundumomi 32 na gabashin kasar awa daya gabanin sauran yankunan kasar. An kuma haramtawa kafofin yada labarai fadin sakamakon ko kuma wallafa shi har sai hukumar zaben ta baiyana hakan tukunna.

Masu sharhi dai na fassara zaben raba gardamar a matsayin zakaran gwajin dafi ko kuma 'yar manuniya ga irin farin jini shugaba Recep Tayyip Erdogan. A wani jawabi da ya yiwa dubban magoya bayansa Erdogan ya zafafa sukar kasashen Turai yana mai cewa zai sake nazarin dangantaka tsakanin Turkiya da kasashen na Turai idan ya yi nasara.

Türkei Referendum Wahllokal in Diyarbakir
Wata mata ke kada kuri'a a zaben raba gardama na TurkiyaHoto: Getty Images/AFP/I. Akengin

Gungun masu son amincewa da kuri'ar raba gardamar domin yiwa kundin tsarin mulkin kwaskwarima wadanda ke samun goyon bayan shugaba Erdogan da Firaminista Binali Yildrim da kuma jam'iyya mai mulki sun mamaye ko ina a kasar a fafutukar jan hankalin jama'a yayin damasu adawa suke fuskantar barazana da rashin basu damar baiyana ra'ayinsu a gidajen Talabijin, sannan da kafafen yada labarai masu goyon bayan gwamnati wadanda su ma suka yi watsi da su. A cewar jam'iyyar adawa ta Republican Peoples Party suna da shaidu kwarara fiye da dari daya na muzgunawa da cin zarafi da ake musu.

Yakin neman zaben dai ya gudana ne karkashin dokar ta baci da aka sanya bayan zargin yunkurin juyin mulkin sojin da bai yi nasara ba a bara.

Wadanda ke goyon bayan amincewa dai na da'awar cewa sauye sauyen da ake so a kawo da za su baiwa shugaban kasar karin karfin iko za su samar da kwanciyar hankali da zaman lafiya a Turkiyya. Yayin da masu adawa kuma ke cewa gyaran kundin tsarin mulkin zai baiwa shugaban kasar karfi ba tare da yi masa linzami ba.

Idan dai aka amince da kuri'ar raba gardamar za'a soke gurbin Firaminista tare da karawa shugaban kasar ikon da Firaministan ke da shi. A saboda haka shugaban kasa zai iya korar ministoci da zartar da dokoki na musamman da kafa dokar ta baci da kuma nada wanda ya ga dama a manyan mukaman gwamnati.