1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben raba gardama a kasar Kenya

November 21, 2005
https://p.dw.com/p/BvKB

A yau alumar kasar Kenya suka kada kuriá jin raáyin jamaá a game da kundin tsarin mulkin kasar na farko tun bayan da kasar ta sami mulkin kai a shekarar 1963. Daftarin kundin tsarin mulkin ya sami goyon bayan sbhugaban kasar Mwai Kibaki. Sai dai a hannu guda an sami rarrabuwar kawuna a dangane da daftarin a tsakanin yan majalisar gudanarwa dama alúmar kasar baki daya, inda a halin da ake ciki arangama tsakanin bangarori biyu da basa ga maciji da juna ya yi sanadiyar mutuwar a kalla mutane tara. Kuriár raba gardamar dai ta zama wata turba ta gwagwarmayar neman ragamar iko tsakanin shugaba Kibaki da yan adawa wadanda suke zargin gwamnatin sa da kasa kabuka komai wajen magance cin hanci da rashawa da kuma akidar nuna kabilanci. Sabon kundin tsarin mulkin ya tanadi sauye sauye masu yawa a ikon da shugaban kasa ke da shi tare da bullo da sabon mukamin P/M mai cikakken iko.