1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben majalisun dokoki a kasar Italiya

April 9, 2006
https://p.dw.com/p/Bv2V

Alúmar kasar Italiya na cigaba da kada kuriá a zaben majalisun dokoki a yau inda ake takara tsakanin Jamíyar raáyin rikau ta P/M Silvio Berlusconi da kuma Jamíyar masu sassaucin raáyin gurguzu karkashin jagorancin Romano Prodi. Manazarta alámuran yau da kullum sun yi hasashen Romano Prodi wanda kawancen jamíyar sa ta kunshi jamíyun mabiya darikar Katolika da masu sassaucin raáyi da kuma yan gurguzu ka iya samun takaitacciyar tazara a bisa abokiyar hamaiyar ta. Binciken raáyoyin jamaá ya nuna kashi 25 cikin dari na masu kada kuriár ba su yanke shawarar wanda zasu kadawa kuriár su ba, wanda kuma kuriár ta su na iya yin tasiri ta kowane bangare. Kimanin mutane miliyan 50 yan kasar Italiyan suka cancanci kada kuriá a zaben wanda zai gudana a yau da kuma gobe litinin. Maáikatar alámuran cikin gida ta kasar Italiya ta baiyana cewa an samar da cibiyoyin zabe guda 60,000 a fadin kasar ga masu kada kuriá.