1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben majalisun dokoki a Israila

March 28, 2006
https://p.dw.com/p/Bv3r

A yau alúmar Israila suka kada kuriá domin zabar sabbin wakilai na majalisun dokoki. Dan takara da ake kyautata tsammanin zai sami rinjaye kuma mukaddashin P/M Israilan Ehud Olmert ya yi alkawarin janye wasu matsugunan yahudawa daga yankin na gabar yamma tare da shata sabuwar kan iyakar Israilan ya zuwa shekara ta 2010. Sai dai kuma baá sami fitowar jamaá ba sosai idan aka kwatanta da zaben da aka gudanar a baya a shekarar 2003. Manazarta alámuran yau da kullum sun baiyana cewa rashin fitowar jamaá ka iya shafar nasarar da jamíyar Kadima ke hangen samu. A waje guda kuma a yayin da Israilawan ke kada kuriá rahotanni sun baiyana cewa mutane biyu sun rasa rayukan su a wani harin roka da yan takifen Palasdinawa suka kai a kusa da yankin zirin Gaza. Kungiyar Isamil Jihad ta baiyana cewa ita ce ke da alhakin wannan hari. A bangare guda kuma Hamas ta ce sakamakon zaben na Israila, ko kada ba zai yi wani tasiri ko ya canza musu raáyi a gabar su da kasar Israila ba.