Zaben Majalisar Turai | Siyasa | DW | 14.06.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zaben Majalisar Turai

A jiya lahadi ne aka gudanar da zaben majalisar Turai, to sai dai kuma yawan wadanda suka shiga zaben bai taka kara ya karya ba

'Yan jam'iyyar The Greens a majalisar Turai

'Yan jam'iyyar The Greens a majalisar Turai

A hakika dai halin da ake ciki a kasar Iraki da fargabar hare-haren ta’addanci hade da matakan garambawul a game da makomar jin dadin rayuwar jama’a, wadannan batutuwa su ne suka fi daukar hankalin mutane a maimakon al’amuran da suka shafi manufofin hadin kan Turai kamar dai daftarin tsarin mulki bai daya ko manufofin noma a zaben majalisar Turai da aka gudanar a kasashe 25 na Kungiyar Tarayyar Turai a jiya lahadi. A wasu daga cikin kasashen, musamman tsaffin membobin kungiyar, masu zaben sun kada kuri’a ne domin bayyana adawarsu ga manufofin Kungiyar Tarayyar Turan baki daya. Shuagabannin da suka fi jin radadin sakamakon zaben kuwa sun hada da P/M Birtaniya da shugaban Faransa da P/M Poland da kuma shugaban gwamnatin Jamus. Masu adawa da manufofin Turai sun shiga doki da murna a kasashen Chek da Poland da Birtaniya a game da sakamakon zaben, wanda suke ganin tamkar wata babbar nasara ce gare su. Babban abin da ya taka rawa ga nasarar wadannan ‚yan kananan jam’iyyun siyasa shi ne karancin mutanen da suka fita domin shiga zaben na jiya lahadi. Wani abin lura kuma shi ne babu wata takamaimiyar doka ko wata ka’ida bai daya ta zaben majalisar Turai kuma a saboda haka bai zama abin mamaki ba kasancewar mutane ba su damu da ainifin manufofin Turai ba sai dai batutuwan dake ci musu tuwo a kwarya dangane da manufofinsu na cikin gida. Su kansu jami’an siyasar dake korafi a game da karancin masu shiga zaben sune ummal’aba’isin wannan koma baya saboda dukufa da suka yi kacokam akan manufofi na cikin gida a yake-yakensu na neman zabe. Babban abin takaici ma shi ne karancin masu shiga zabe fiye da kima da aka fuskanta a sabbin membobin Kungiyar Tarayyar Turai a gabacin nahiyar. Jami’an siyasar wadannan kasashe sun gaza wajen wayar da kan al’umarsu a game da muhimmancin wannan zabe ga kasa baki daya. ‚Yan mazan jiya dai zasu ci gaba da rinjayensu a majalisar, sai kuma ‚yan Socialdemocrats da zasu biyo baya. Mai yiwuwa a samu baraka tsakanin magoya-baya da masu adawa da manufofin Turai a tsakanin ‚yan mazan-jiyan, lamarin da zai gurgunta rinjayen da suke da shi a majalisar, wacce bata da jibantar wata gwamnati ta tsakiya bai daya tsakanin kasashen Turai. Mai yiwuwa hakan ne ya sanya al’umar kasashen nahiyar ba su dauke ta da muhimmanci ba, saboda ba magana take yi da yawunsu ba, bisa sabanin yadda lamarin yake dangane da majalisun dokoki na cikin gida. To sai dai kuma wannan ci gaba na bijire wa zabubbuka ba nahiyar Turai ce kadai ke fama da shi ba, hatta kasa kamar Amurka tana fama da irin wannan koma baya tun kuwa abin da ya kama daga karshen shekarun 1970. Akalla dai nadin majalisar yana da muhimmanci a maimakon a kyale mabiya dogon Turanci su rika cin karensu babu babbaka a Brussels, shelkwatar Kungiyar Tarayyar Turai.