Zaben Majalisar Turai A Ranar Lahadi Mai Zuwa | Siyasa | DW | 09.06.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zaben Majalisar Turai A Ranar Lahadi Mai Zuwa

A ranar lahadi mai zuwa ne za a gudanar da zaben majalisar Turai mai wakilai 732, wacce kuma take taka muhimmiyar rawa a zartaswar Kungiyar Tarayyar Turai

Akwatunan zaben majalisar Turai

Akwatunan zaben majalisar Turai

Sakamakon wani binciken ra’ayin jama’a da aka gudanar dangane da zaben majalisar Turai da za a gudanar ranar lahadi mai zuwa duka-duka kashi 40% na masu ikon kada kuri’u a nan Jamus ne suka bayyana niyyarsu ta halartar rumfunan zaben. Kuma da yawa daga cikinsu, ba saboda manufofin kungiyar ne zasu jefa kuri‘ar tasu ba. Zasu yi hakan ne dangane da manufofin gwamnati a fadar mulki ta Berlin. Bisa ga ra’ayin wadannan mutane, babban abin dake ci musu tuwo a kwarya shi ne manufofi na cikin gida, amma ba rawar da majalisar Turai ke takawa ba. Ta la’akari da haka goyan baya ko rashin goyan baya da wakilan jam’iyyar SPD zasu samu a zaben ya danganta ne da salon kamun ludayin gwamnatinta ta hadin guiwa da jam’iyyar the Greens, amma ba rawar da wakilanta ke takawa a majalisar Turai ba. Hakan ya sanya jam’iyyar CDU ke tattare da ra’ayin cewar sakamakon zaben na ranar lahadi zai iya zama gargadi ga gwamnatin hadin guiwar ta SPD da The Greens domin ta canza salon kamun ludayinta. Ita kuma SPD a nata bangaren ta sake gabatar da manufar adawarta da yakin Iraki domin zama turbar yakinta na neman zaben. To sai dai kuma ko da yake ba shakka wannan magana tana da muhimmanci hatta a wannan lokaci da muke ciki yanzun, amma ba ta da wata rawa ta a zo a gani da take takawa dangane da zaben majalisar Turai. A tsakanin illahirin jam’iyyun, The Greens ce kawai ta canza sibgar yakinta na neman zabe tana mai mayar da hankalinta kacokam akan makomar Turai baki daya da kuma yin kiran mayar da batutuwan kare kewayen dan-Adam wata manufa bai daya tsakanin kasashen nahiyar. A dai halin da ake ciki yanzun an shiga wani sabon yanayi ne, inda batutuwa na kasa baki daya su kan dauki hankalin jama’a a yakin neman zabe, abin da ya hada har da zabubbuka na jiha, a nan Jamus. Ta la’akari da haka bai zama abin mamaki ba kasancewar hatta zaben na majalisar Turai ya zama tamkar mizani game da yadda mutane ke nakaltar manufofin gwamnati. To sai dai kuma kamar yadda muka yi bayani tun farko mutane ba sa sha’awar halartar rumfunan zaben kuma aka shiga wani yanayi na rowar kuri’a. Dangane da masu halartar rumfunan kuwa burinsu shi ne su ja kunnen gwamnati domin ta canza salon kamun ludayinta. Wannan manufar ba shakka ita ce zata taka muhimmiyar rawa dangane da zaben majalisar Turan a ranar lahadi mai zuwa.