Zaben kwararrun yan majalisa aIran | Labarai | DW | 16.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben kwararrun yan majalisa aIran

Sakamakon zaben kwarraun yan majalisar dokoki a Iran na nuni dacewa tsohon shugaban kasar Akbar Hashemi-Rafsanjani,shine ke da rinjayen kuriu,ayayinda dan takara dake da alaka da shugaba Ahmedinejad ,yana matsayi na 6,a jerin sauran yan takara.Rafsanjani dake zama daya daga cikin manyan masu adawa da shugaba Mahmoud Ahmadinejad ,na wakiltan hadin gwiwar jammiyyun masu sassaucin raayi da masu neman sauyi ne a majalisar kwararrun ,ayayinda Mohammad –Taqi Mesbah Yazdi ke wakiltan bangaren shugaban kasar.Wannan majalisar wakilai kwararru dai nada ikon nadi,lura da sauke shugaban addini Ayatollah Ali Khamenei,wanda shine mutumin dake da karfin ikon zartar da hukuncin karshe ,adangane da dukkan lamura na kasa.