Zaben Kenya | Labarai | DW | 28.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben Kenya

Shugaban Adawa Raila Odinga,ne ke jagoranci da mafi yawan kuriu fiye da abokin takarar sa Mwai Kibaki ,bisa ga yawan kuriu, da aka kidaya a zaben shugaban kasar Kenya daya gudana a jiya.Bisa ga rahotannin kafofin yada labaran Kenyan dai ,ayayinda ake cigaba da kidayan kuriun Dan Adawa Odinga yana da kuriu sama da million biyu ayayinda Kibaki ya doshi million daya da rabi.idan har shugaban Adawan ya lashe zaben a karshe,Shugaba Mwai Kibaki zai kasance shugaban kasa na farko da aka sauke daga mulki ta hanyar zabe,da samunb yancin kann kasar.Jamian tsaro kuwa na taka rawa wajen tabbar da cewar komai ya tafi cikin luman kamar yadda shugaban rundunar yansanda General Hussain Ali ya shaidar.