Zaben kasar Zambia | Labarai | DW | 25.09.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben kasar Zambia

Shekaru biyar bayan kasancewa shugaban kasar Zambia a jere har sau uku,shugaba Levy Mwanawasa wanda zai sake yin takara ya amince dacewa,kawo yanzu matsalolin kasar kalilan ne ya samu warwarewa,A dai dai lokacin da alummar Zambia kimanin million 3.9,da suka cancanci zabe ke shirin zuwa runfunan zabe a ranar alhamis,Mwanawasa mai shekaru 59 da haihuwa na fatan cewa,fadin gaskiya dangane da halin da kasar ke ciki a karkashin mulkinsa,zai taimaka masa wajen samun daman lashe wannan zabe a karo na biyu kuma na karshensa akan wannan karaga.Duk dace babu wani sahihin sakamakon jin raayin jamaa,bisa dukkan alamu shugaban zambian na yanzu,wanda ya hau karagar mulki a shekarata 2001 d,da yawan kuriu kashi 28 daga cikin 100 kachal,baya fuskantar wata barazana na faduwa,musamman a bangaren mai kalubalantarsa daga jammiyar adawa ta popular front,Michael Sata,da Hakainde Hichilema.A taron sa na yakin neman zabe a mahaifarsa dake Ndola,Mwanawasa ya fadawa magoya bayanshi cewa an samu raguwar yawan wadanda ke rayuwa cikin kunci na talauci daga kashi 80 daga cikin 1200 ,zuwa kashi 65,ayayin mulkinsa.

 • Kwanan wata 25.09.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5I
 • Kwanan wata 25.09.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5I