1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben kasar Saleon

Zainab A MohammedAugust 10, 2007

A gobe ne zaa gudanar da zaben kasa baki daya a Saleon..

https://p.dw.com/p/Btuk
Birnin Freetown
Birnin FreetownHoto: AP

A ranar Alhamis data gabata ne dai bangarori uku na tuntuba dangane da makomar yankin Serbiawa na koso suka gana a birnin London kafin su wuce izuwa birnin Belgrade dake zama babban birnin Serbiayawan a ranar Jumaa.

Kungiyar tuntuban juna data hadar da Amurka da Rasha da kungiyar tarayyar Turai Eu,sun karbi harkokin sasantawa a yankin,a wantan daya gabata nedai,bayan da kudurin samarwa kosovo yanci wanda kasashen yammaci suka marawa baya yasha kaye, a majalisar dunkin duniya,saboda Rasha ta hau kujerar naki , amadadin abokiyarta Serbia.

Wannan kuduri dai yazo ne bayan mahawarar warware wannan takaddama ta ci tura cikin watanni 13 da aka aka tabka ana yi.

A shekaru 8 da suka gabata dai mdd ce ke lura da lamuranm yankin na kosovo,bayan da gamayyara dakarun kasashen yammaci suka shiga tsakani a shekarata 1999,domin ceto rayukan yan kabilar Albaniyawa kimanin million 2 ,daga hannun dakarun serbia ,a karkashin mulkin maarigayi Slobadon Milosevic.

A ranar jumar data gabata nedai bangarorin guda uku suka je babban birnin yankin sabiyawan na Belgrade inda suka tattaunawa ,koda yake kawo yanzu babu alamun cimma wani tudun dawafawa a wannan yunkuri da aka sanya gaba.

Jakadana kungiyar gamayyar turai a wannan ayari Wonfgang Ischinger yace zasu cigaba da kori wajen ganin cewa an shawo kan wadanda ke adawa da shirin ….

“Yace abu mawuyaci ne gano bakin zaren warware wannan matsala,sai dai fata muke cewa dukkan bangarorin yankin da Amurka da kasashen turai da Rasha su gabatar da manufar su guda daya akan yankin,ta haka ne kadai zaa iya cimma tudun dafawa”

A shekara ta 2006 data gabata nedai aka fara tattaunawa dangane da makomar yankin,lokacin kasashen turai suka cewa bazasu cigaba da kulawa da yankin na din din din ba.Amurka ta bukaci a gabatar da kuduri a shekarar data gabata ,kuma bisa dukkan alamau har yanzu babu alamun zaa cimma wani kuduri zuwa karshen wannan shekara a kan makomar yankin na kosovo.Kamar yadda Mr Ischinger yayi nuni dashi

“Yace duk da kokarin da akeyi na ganin cewa an cimm madafa,idan Amurka da Rasha basufito fili sun taka rawar gani,babu alamun cewa wannan ayari guda uku na tuntuba zai cimma wani tudun dafawa”

To sai dai a ganin Franz Lothar Altmann dake zama masani kan harkoki siyasa da kimiyya shigar Berlin na iya samun matsala da washinton adaangane da batun Rasha..

“ ayayinda gwamnati a Berlin ke kokarin ganin cewa ta janyo Rasha domin warware wannan matsala,hakan na iya haifar da baraka cikin dangantakarta da Amurka”.