1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zaben kasar Kongo

Shugaba Kabila ya ba da sanarwar niyyarsa ta tsayawa takara

Shugaba Kabila

Shugaba Kabila

A hukumance dai shugaba Joseph Kabila ya ba da sanarwar shirinsa na shiga takarar zaben kasar Kongo, wanda za a gudanar a tsakiyar watan yuni mai zuwa. Kawo yanzu ‘yan takara 13 ne suka yi rajista a cewar wata sanarwa ta hukumar zaben kasar. To sai dai kuma an ji wani kakakin shugaba Kabila yana fadi ta gidan telebijin cewar shugaban zai tsaya takara ne da suna illahirin al’umar kasar Kongo a saboda haka ba ya bukatar wata jam’iyya ta siyasa. Kawo yanzun dai wata jam’iyya mai taken jam’iyyar sake gina kasa da tabbatar da demokradiyya, ita ce ke rufa wa Joseph Kabila baya. Dubban magoya bayan jam’iyyar Social-Democrats ta dan hamayya Etienne Tshisekedi suka shiga zanga-zanga domin ganin lalle sai an kara wa’adin rajista akan ranar 23 ga wata da aka tsayar. Shi dai Tshisekadi tun bayan samun ‘yancin kan kasar Kongo a shekarar 1960 ake damawa da shi a dukkan gwamnatocin da aka yi a kasar, kuma sau uku yana rike mukamin piraminista. Amma kuma a daya hannun ya sha fuskantar muzantawa daga dan kama karya Mobutu Sese Seko da Laurent Kabila, mahaifin Joseph kabila da aka yi wa kisan gilla. Tsofon dan siyasar na bukatar ganin an ba wa ‘yan hamayya wata cikakkiyar dama ta taka muhimmiyar rawa a shirye-shiryen zaben da kuma lokacin gudanar da shi.

Shi ma Azarias Ruberwa daya daga cikin mataimakan shugaba Kabila a gwamnatin wucin gadi ta hadin gambiza na tattare da ra’ayin cewar wajibi ne a kara wa’adin saboda ranar da aka tsayar din ba zata wadatar ba. Wasu majiyoyin ma cewa suka yi kawo yanzu wakilai 50 ne kacal daga cikin wakilan majalisar kasar ta Kongo su 500 suka yi rajista kuma a sakamakon haka jam’iyyar RCD ta Azarias Ruberwa tayi barazanar kaurace wa zaben. Shuagabannin ‘yan tawaye hudu ne ke da kujera a majalisar ministocin gwamnatin kabila kuma suna fargabar yin watsi da makomarsu sakamakon zaben. Ta la’akari da haka ne sakatare-janar na MDD Kofi Annan, a tattaunawar da ya gudanar a Kinshasa yayi alkawarin cewar sojan kiyaye zaman lafiya su kimanin dubu 17 da majalisar ta tsugunar a Kongo zasu ci gaba da wanzuwa a kasar bayan zaben. Sojojin zasu samu rufa baya daga dakarun kwantar da tarzoma su 1500 da Kungiyar Tarayyar turai zata tura, wadanda za a danka musu alhakin tsaron zaman lafiya fadar mulki ta Kinshasa da kewayenta. Kungiyar ta taba tura sojojinta zuwa kasar ta Kongo karkashin tutar MDD a shekara ta 2003, inda sojan Faransa suka murkushe dakarun sa kai a Bunia tare da ba da cikakkiyar kariya ga sansanonin ‘yan gudun hijira da filin saukar jiragen saman yankin.