Zaben kasar Kongo | Siyasa | DW | 11.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zaben kasar Kongo

A daidai lokacin da ake shirin gudanar da zabe a kasar Kongo al'umar kasar na fama da matsalolin rayuwa

Unguwar lingwala na daya daga cikin tsaffin unguwanni a birnin Kinshasa kuma daya daga cikin unguwanni masu fama da talauci a birnin yanzu haka. An yi shekaru da dama ba wani jami’in siyasar dake sha’awar saka kafa a unguwar. Duk inda mutum ya waiwaya zai tarar da dalar shara da suka barbazu a yankin. Kazalika unguwar bata da wata nagartacciyar hanya ta kawar da najasa. Ta la’akari da haka bai zama abin mamaki ba kasancewar mazauna unguwar ta Lingala suna ko oho da hoton yakin neman zabe na shugaba mai ci Joseph Kabila da aka mammanna a gefen tituna.

“Matsalolinmu na da yawa matuka ainun. Kamar yadda ake gani dukkan titunan sun lalace ga dalar shara ta barbazu ko’ina ga karni da warin najasa, kuma mutane ba su da ruwan sha mai tsafta. Mutane na fama da matsaloli na rayuwa saboda ba sa samun albashinsu akan kari. Walau sojoji ko ‘yan sanda da sauran kananan ma’aikata. Ta yaya wadannan mutane zasu iya ci da iyalansu. A sakamakon haka ne yara da yawa suka tagayyara saboda iyayensu sun koresu daga gida domin basu da ikon kula da su. Hada-hadar zaben dai tana tafiya salin-alin amma babu daya daga cikin ‘yan takarar dake magana da yawun talakawa.”

A hakika kuwa tun bayan samun ‘yancin kan kasar Kongo daga hannun Turawan Belgium, kasar bata taba samun wani sahihin tsarin mulki na demokradiyya ba, sai dai mulke-mulke na kama karya da tsabar son kai daga jami’an siyasarta irinsu Mobutu Sese-Sekou. Shi ma shugaba Laurent Kabila da ya biyo baya bai haifarwa da kasar da alheri ba daidai da dansa Joseph Kabila da ya gaje shi. Dukkansu jirgi daya ne ke dauke da su. Dukkansu sun durmuyar da kasa a cikin wata mummunar al’ada ta cin hanci da son kai. Hakan na daya daga cikin dalilan da suka sanya mutane ba su dokata da zaben ba, kamar yadda aka ji daga wani da ake kira Mavola Monongo, wanda ya ce faufau shi kam ba zai fita kada kuri’a ba, kai ko rajista ma bai yi ba, saboda kamar sauran ba zauna yankin Lingwala, bai yarda da shuagabannin kasar ba, abin da ya hada har da wadanda za a zaba a ranar 30 ga wata. Ya kara da cewar:

“A gani na jami’an siyasa ba zasu iya tsinana mana kome ba. Taimako sai daga Allah kawai.”