1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben kasar Indonesiya

April 8, 2004

Sai a karshen watan afrilu ne ake sa ran samun cikakken sakamakon zaben kasar Indonesiya

https://p.dw.com/p/Bvkr
Megawati a yakin neman zabe
Megawati a yakin neman zabeHoto: AP

A misalin shekaru shida da suka wuce ne aka shimfida turbar mulkin demokradiyya a kasar Indonesiya, wacce tafi kowace yawan Musulmi a duniya, bayan kifar da mulkin shugaba Suharto. Mulkin na demokradiyya ya samu kyakkyawar nasara idan aka kwatanta da yadda al’amura suka kasance a zamanin baya. A baya ga zaben majalisar dokoki, an kuma kada kuri’a domin nada wakilan sabbin majalisun jiha da aka kirkiro. Sai kuma zabe na lardunan kasar 32 da kananan hukumomi kimanin 400. Yakin neman zaben an gudanar da shi ne ba tare da wata tangarda ko daukar hankalin jama’a ba. A yayinda a zamanin baya mutane kan dokata da zabubbukan da aka shirya, ga alamu a wannan karon munarsu ce ta koma ciki a game da dogon burin da suka saka a zuciyarsu bayan kifar da gwamnatin shugaba Suharto. Babu wani daya daga cikin jam‘iyyun dake takarar neman zaben dake da wani takamaiman shiri na tinkarar matsalolin cin hanci da tabarbarewar tattalin arzikin da Indonesiya ke fama da shi. Ko da yake wannan matsala ce da ta zama ruwan dare a duniya. Sakamakon dai da aka samu daga zaben ya zuwa yanzu ya nuna yadda mutane suka yi taka tsan-tsan tare da yin sara suna duban bakin gatarinsu dangane da jam‘iyyun da zasu ba wa goyan baya. Kuma ko da yake al’umar kasar na kewar zamanin mulkin Suharto da ya wanzu karkashin wani yanayi na yalwa da wadatar tattalin arziki iya gwargwado ga jama’a, amma goyan baya na kashi 20% ba zai iya sake mayar da hannun agogo baya domin sake komawar jam'iyyar Suharto kan karagar mulki ba. Ita kuwa jam’iyyar shugaba Megawati ba ta cika alkawururrukan da tayi a zaben da ya gabata ba, ko da yake shugabar har yau tana da farin jini tsakanin jama’a. Megawati ta gaza wajen shawo kan matsalolin tattalin arzikin kasar da kuma rikice-rikicen da ake fama da su a wasu lardunanta, musamman ma a lardin Aceh. Dangane da manazarta al’amuran Indonesiya a kasashen ketare dai, babban abin da suka fi mayar da hankali kansa shi ne nasarorin jam’iyyun addini a zaben. Wannan lamarin ya fi ci wa Amurka tuwo a kwarya saboda tsoro da take yi na cewar mai yiwuwa Indonesiya ta zama wani sansanin kungiyar Al’ka’ida da sauran kungiyoyi masu tsananin kishin addini. Amma abin lura shi ne kasancewar ko da yake a cikin shekarun baya-bayan nan al’umar indonesiya sun kara karkata zuwa ga addini, suna masu biyayya ga al’amuran Musulunci sau da kafa, amma jam’iyyu masu akidar addini ba su taka wata rawa ta a zo a gani a siyasar kasar. Dalilin haka kuwa shi ne su kansu sauran jam’iyyun suna karkashin jagorancin shuagabanni ne Musulmi dake biyayya ga addini, amma kuma a daya bangaren suna kaunar ganin an yi zama na cude-ni-in-cude-ka da sauran al’umar kasar dake bin wasu addinan dabam kamar yadda aka saba hakuri da juna tsakaninsu tun a zamanin kakannin-kaka. Ta la’akari da haka wajibi ne a yaba wa kasar ta Indonesiya a matsayin kasa ta uku mafi girma dake bin tsarin mulki na demokradiyya tsantsa a duniya.