ZABEN KASAR INDIA YA FARA FITOWA: | Siyasa | DW | 13.05.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

ZABEN KASAR INDIA YA FARA FITOWA:

Hausawa dai kance rana bata karya sai dai uwar diya taji kunya,a yanzu haka sakamakon zabubbukan yan majalisun dokoki na kasar India da aka gudanar a tsawon mako uku ya fara fitowa a tun daga jiya laraba.

Sakamakon zaben a yanzu haka ya nunar da cewa jamiyyar adawa da Sonia Ghandi kewa jagoranci ce ta samu nasarar da ba a zata ba a can baya kuma da alama a nan gaba ana ganin jamiyyar tace zata kafa gwamnati.

A can baya dai bayanai sun shaidar da cewa jamiyyar BJP ta faraminista Atal Behari Vajpayee ce zata lashe zaben yan majalisun dokokin da gagarumin rinjaye amma bisa wasu dalilai da masu nazarin siyasar kasar ke gani jamiyyar ta samu koma baya.

Wan nan rashin cikkakkiyar nasara da jamiyyar ta BJP tayi ministan tsaro na kasar ya shaidar da cewa ka iya tursasawa faraminista Vajpayee yin murabus daga mukamin sa tare da barin jamiyyar sa ta Hindu ta kasance jamiyya mai adawa da jamiyyar da zata kafa gwamnati.

A ata bakin Pran chopra wani mai nazarin abubuwan da kaje yazo a kasar cewa yayi kayen da jamiyyar ta faraminista ta fara fuskanta nada nasaba da irin matakan kwaskwarimar tattalin arziki da gwamnatin ta dauka a hannu daya kuma da watsi da al,amurran mutanen kasar,wanda hakan ya jefa miliyoyin yan kasar cikin hali na kaka ni kayi da kuma talauci.

Gwamnatin ta Vajpayee a cewar Pran chopra tafi mayar da hankali ne ga gudanar da aiyuka a birane a maimakon a yankuna yankuna da kuma kauyuka kauyuka inda ilahirin talakawan kasar ke zaune.

Shi kuwa B.G Verghese cewa yayi abin da ya faru da jamiyyar ta BJP ba wani abu bane illa abin nan da hausawa kance dan hakin daka raina shi yake tsone maka ido.

A can baya a cewar mai sharhin abin da kaje yazon jamiyyar faraminista Vajpayee tayi sakaci wajen daukar matakan daya kamata bisa zargin cewa ita Sonia Ghandi mutuniyar kasar irtaliya ce a don haka zasu samu nasarar cin zabe ba tare da wata wahala ba,tare da mance cewa ba a nan gizo yake sakar ba.

Mr Verghese yaci gaba da cewa ita kuwa Sonia Ghandi a maimakon ta hana hannu da gwiwa sai tayi amfani da damar da take da ita wajen kusantar mata yan uwanta dake kasar wanda ta haka ne a cewar sa jamiyyar tata ta bawa marada kunya a wadan nan zabubbuka na yan majalisar dokokin.

Bugu da kari a cewar Mr Verghese akwai kuma zargin cewa gwamnatin Vajpayee tayi sakaci wajen daukar tsauraran matakan daya kamata wajen shanyo kann rikici na iyaka dake tsakanin su da makociyyar kasar wato Pakistan.

Wan nan a cewar masu nazarin abin da kaje yazon ya kuma taimaka wajen samun nasarar jamiyyar ta Sonia Ghandi a wan nan karon.

Rahotanni dai daga kasar sun shaidar da cewa nan bada dadewaba idan sakamakon zaben ya kammala fitowa kuma nasara ta tabbata ga jamiyyar Sonia Ghandi to babu makawa itace zata dare kann kujerar faraministan kasar ta India.

IBRAHIM SANI.