1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben Jihar NRW ranar lahadi

May 20, 2005

A ranar lahadi za a gudanar da zaben jihar Northrhine-Eastfalia dake nan Jamus. Sakamakon zaben zai zama mizani a game da makomar mulkin hadin guiwa na SPD da The Greens a Berlin

https://p.dw.com/p/Bvbm
Rüttgers da Steinbrück dake takarar mukamin gwamna a zaben jihar NRW dake nan Jamus
Rüttgers da Steinbrück dake takarar mukamin gwamna a zaben jihar NRW dake nan JamusHoto: AP

A yakinta na neman zabe jam’iyyar SPD ta fito fili ta bayyana cewar ita kam ba zata cika baki ba, ba zata yi wa jama’a wasu alkawururrukan da ba zata iya cika su ba, inda shi kansa Peer Steinbrück, gwamnan jihar Northrhine-Westfaliya, kuma dan takarar jam’iyyar ta SPD yake cewar ba zai iya yi wa mutane alkawarin samar da sabbin guraben aikin yi ba, amma fa bai dadara ba yana mai gwagwarmaya a kowace rana ta Allah domin ganin al’amura sun daidaita a jiharsa. Kazalika ya ce ba zai yi kari akan abin da gwamnatinsa ta saba kashewa ba, illa a fannin ilimi kawai. Babu wani dalibi a nan jihar ta Northrhine-Westfaliya da zai biya kudin makaranta a jami’o’inta, matsawar da yake kann mukaminsa na gwamna a karkashin tutar SPD. Maganar kudaden karatu a jami’a na daya daga cikin batutuwan da suka fi daukar hankali a yakin neman zaben jihar ta Northrhine-Westfaliya, sai kuma matsalar nan ta rashin aikin yi dake addabar jihar. A yayinda SPD da The Greens ke adawa da manufar biyan kudin makarantar, su kuma jam’iyyun FDP da CDU na ba wa manufar goyan baya. Jigon jam’iyyun biyu a yakinsu na neman zabe shi ne, gusar da dogon turanci. Jam’iyyun na FDP fa CDU sun yi alkawarin soke wasu dokoki da ka’idoji masu tarin yawa in har sun cimma nasarar zaben ta yadda za a rage bin wasu manufofi na dogon turanci, wanda a ganinsu hakan zata taimaka a samar da karin guraben aiki ga jama’a. An saurara daga bakin dan takarar CDU Jürgen Rüttgers yana mai bayani da cewar wajibi ne a saukake wa ‚yan kasuwa hanyar zuba jari ta yadda jama’a zasu samu guraben aikin yi. Wannan dai shi ne karo na biyu da jami’in siyasar ke yunkurin darewa kann kujerar gwamna a jihar Northrhine-Westfaliya. A karon farko a misalin shekaru biyar da suka wuce ya kwashi kashinsa a hannu, amma a wannan karon yana fata ne cewar bayan mulki na tsawon shekaru 40 a yanzu mutane sun gundura da salon kamun ludayin SPD kuma zasu dawo daga rakiyarta domin goya wa CDU baya. Da dai takarar zata kasance ne tsakanin Jürgen Rüttgers da Peer Steinbrück kai tsaye, ba tare da tutar wata jam’iyya ba, to kuwa da a wannan karon ma jami’in siyasar na CDU ba zai kai labari ba, saboda abokin takarar tasa daga jam’iyyar SPD ya fi shi farin jini matuka ainun a tsakanin jama’a, kamar yadda bincike ya nunar. Ita kuwa jam’iyyar FDP a yakinta na neman kuri’a ta mayar da hankali ne wajen kalubalantar manufofin gwamnati wajen tallafa wa ayyukan hakar kwal da makudan kudi, wanda take ganin tsofon yayi ne. Abu mafi alheri a ganinta shi ne daukar karin malamai domin cike gibin da ake fama da shi a makarantun jihar. Ita kuma The Greens, kamar yadda aka saba, maganar kare kewayen dan-Adam shi ne a’ala a gareta, kuma a saboda haka ta fi mayar da hankali ga fasahar samar da makamashi maras illa ga makomar dan-Adam, manufar da ta ce tana taimakawa wajen samar da guraben aikin yi ga jama’a. A takaice dai kamar yadda muka yi bayani tun farko wannan zaben na da muhimmanci a matsayi na kasa baki daya saboda sakamakonsa zai zama mizani game da makomar gwamnatin hadin guiwa ta SPD da The Greens, domin jihar Northrhine-Westfaliya ita ce kadai ta rage a hannun jam’iyyun guda biyu a tsakanin illahirin jihohin kasar nan su goma sha shida.