Zaben Jihar NRW ranar lahadi | Siyasa | DW | 23.05.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zaben Jihar NRW ranar lahadi

A sakamakon rashin nasarar zaben da aka gudanar a nan Jihar Northrhine-Westfaliya a jiya lahadi, jam'iyyar SPD na fatan ganin an gudanar da zaben majalisar majalisar dokoki na gaba da wa'adi a cikin wannan shekarar

Sanarwar da aka bayar a game da sabon zabe na gaba da wa’adi a nan Jamus ta zo wa kungiyar tarayyar Turai a ba zata. Domin kuwa a yanzun al’amura zasu tsaya ne cik har sai an kammala wannan zabe. Gwamnatin hadin guiwa ta SPD da The Greens ba zata tsoma baki domin tsayar da wasu shawarwari masu muhimmanci dangane da makomar kungiyar ba. Da wuya a cimma daidaituwa a sabanin da ake a game da kasafin kudin Kungiyar ta Tarayyar Turai wanda ya shafi tsawon lokaci har ya zuwa shekara ta 2013 da kuma kai ruwa ranar da ake famar yi dangane da yawan gudummawar da Jamus ke bayarwa ga baitul-malin kungiyar. A ganawar da aka gudanar tsakanin ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar a Brussels, jiya lahadi, ba a cimma tudun dafawa ba tsakanin kasashen dake ba da gudummawa mafi tsoka, da kuma kasashen dake cin gajiyar gudummawar. An ji daga bakin ministan harkokin wajen Luxemburg Jean Asselborn yana mai fadin cewar sabon zabe na gaba da wa’adi da za a gudanar a Jamus zai kara tsaurara lamarin. Ita kuma kantomar KTT akan al’amuran kudi Dalia Grybauskaite nuni tayi da cewar wajibi ne dukkan gwamnatocin da lamarin ya shafa su ba da la’akari da irin alhakin da ya rataya wuyansu ko da kuwa suna karkashin wani yanayi ne na yakin neman zabe. Bisa ga dukkan alamu kuwa manufofin kungiyar tarayyar Turai zasu zama wani bangare na batutuwan da zasu dabaibaye yanayin yakin neman zaben, misali fargabar da Jamusawa ke yi na dauko leburori masu rafusan albashi daga kasashen gabacin Turai domin aiki a nan kasar. Kazalika sauran batutuwan da suka shafi ka’idojin aiki da ake fatan danka alhakinsu a hannun KTT. An dai shirya fara shawarwarin karbar karin kasashe a kungiyar a ranar 3 ga watan oktoba mai zuwa, amma masu ra’ayin rikau a nan Jamus a karkashin jagorancin Angela Merkel, wacce mai yiwuwa nan gaba ta zama shugabar gwamnatin Jamus, suna adawa da karbar kasar Turkiyya. Tuni jam’iyyar CSU ta jihar Bavariya ta ce, maganar karbar Turkiyya na daga cikin batutuwan da zata mayar da hankali kansu a yakinta na neman zabe. Wani abin da manazarta al’amuran diplomasiyya ke fargaba game da shi kuma shi ne yiwuwar gurguncewar al’amuran KTT baki daya, idan har kasashen Faransa da Netherlands suka yi fatali da daftarin tsarin mulkin kungiyar, hade da sabon zabe na gaba da wa’adi a nan Jamus. Nasarar CDU a zaben zata ba wa masu ra’ayin mazan-jiya rinjaye a majalisar Turai. A sakamakon mawuyacin hali na dardar da ake ciki a Berlin ministan tsaro Peter Struck da ministan harkokin waje Joschka Fischer da dai sauran ministocin da al’amura suka shafa, ba su halarci tarurrukan majalisun ministocin da ake gudanarwa yanzu haka a birnin Brussels ba.