1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben Italiya: Rikicin tattalin arziki da na kudi

Mohammad Nasiru Awal SB
March 2, 2018

Har yanzu bankuna a kasar Italiya na fama da yawan basussuka, ita ma gwamnatin kasar bashin ne ya yi mata katutu a daidai lokacin ke shirin gudanar da zabe a ranar 4 ga watan nan na Maris.

https://p.dw.com/p/2tbmT
Italien Rom Wahlplakate
Hoto: picture-alliance/NurPhoto/A. Ronchini

Bankuna a birnin Siena na daga cikin bankunan kasar Italiya da ke fama da matsala bashi, to sai dai ministan kudin kasar ta Italiya, Pier Carlo Padoan, wanda dan yankin ne kuma yake wakiltar mazabar yankin, ya ce matsalar ba ta kai yadda ake yayatawa ba, yana mai cewa ba za ta shafi masu zabe ba.

Yankin Siena shi ne mazaunin bankin Monte dei Paschi mafi dadewa a kasar da aka kafa a shekarar 1472 a matsayin cibiyar ba wa talakawa da masu karamin karfi bashi. A 2016 bankin ya kusan durkushewa saboda dinbim bashi, amma yanzu ya farfado bayan da gwamnati ta tallafa masa.

Da sauran rina a kaba dangane da matsalar basassuka

Italien Wahlkampf 2018 | Stammhaus der Bank Monte dei Paschi in Siena
Babban ginin asali na Bankin Monte dei Paschi a Siena Hoto: picture alliance/Arco Images/F. Schneider

A yankin na Siena inda matsalar bankunan Italiya ta samo tushe, ministan kudin kasar Pier Carlo Padoan ke takara neman kujerar majalisar dokokin kasa. Shi dai ministan aka dorawa nauyin ceto bankuna da ya ce yanzu an fara samun haske.

"Hasashen da aka yi ta yi cewa Italiya za ta ruguje saboda matsalolin bashi bai tabbata gaskiya ba. Italiya ta tsaya kan kafarta. Hakika muna fama da dinbim basussuka, amma sun fara ja da baya, kasar tana samun bunkasa tana kuma ba da gudunmawa wajen daidaita al'amura a tsakanin kasashen masu amfani da kudin Euro. Hakan kuwa saboda matakan da gwamnati ta dauka. Ba na ganin wata matsalar bankuna a Italiya yanzu."

Sai dai ministan da ke yakin neman zabe bai ce uffan ba game da wasu bankunan da ke dab da durkusehwa, muhimmin batun da Ruggero Bertellui farfesa a fannin tattalin arziki a jami'ar birnin Siena ya yi korafi cewa bai taka rawa gabanin zaben a Italiya.

"Abin bakin ciki ne yadda jam'iyyun siyasa ba su saka batun basassukan bankunan a cikin shirye-shiryensu ba. Manufarsu ita ce watsi da batun. Amma dole ne bayan zaben a kulla kawance. Dole ne mu yi aiki don inganta abubuwa domin yana da muhimmanci mu tsare dan ci gaban da muka samu."

Kananan bankuna sun yi yawa

Yanzu haka dai tattalin arzikin Italiya ya fara bunkasa kuma matsalar rashin aikin yi ta ragu, amma har yanzu akwai matsaloli na tsare-tsare da ba a kai ga magance su ba. A saboda haka ne Farfesa Bertellui ya ce dole a hade kananan bankuna sannan a rufe rassan bankuna da yawansu ya wuce kima domin a rage kashe kudi.

Finanzminister italiens Pier Carlo Padoan
Ministan kudin Italiya Pier Carlo PadoanHoto: Getty Images/AFP/G. Bouys

Dan takarar jam'iyyar 5-Star Movement, Leonardo Franci, wanda kuma masani ne na harkokin kudi shi zai fafata da ministan kudin Italiya Pier Carlo Padoan, ya ce har yanzu ba a warware matsalar basussukan ba, yana mai cewa ba daidai ba ne gwamnati ta ci gaba da tallafa wa bankuna.

"Karin yawan kudin da gwamnati ke kashewa ba mataki ne da ke kan kyakkyawar hanya ba. Karin yawan shekaru yin ritaya ba shi daidai. Watakila karin kashe kudi na da kyau don dadadawa masu zabe, amma a karshe hakan ba za ta tabbata ba."

Masana sun ce rage bashin da ke kan kasar ta Italiya zai yiwu ne idan tattalin arzikin kasar ya ci gaba da bunkasa. Sai dai yanzu bunkasa tana kashi daya cikin 100, da ke zama mafi kankanta a tsakanin kasashe masu amfani da kudin Euro.